Gwamna Lawal Ya Kafa Tarihi da Jirgin Farko na Maniyyata Ya Tashi zuwa Kasar Saudiyya
- Gwamnan Dauda Lawal ya kafa tarihi da ya gina filin jirgin sama na kasa da kasa, irinsa na farko a tarihin jihar Zamfara
- Jirgin kamfanin Max Air ya kwashi tawagar maniyyata na farko daga jihar Zamfara zuwa kasar Saudiyya a jiya Juma'a
- Gwamna Lawal ya nuna tsantsar farin cikinsa kasancewar maniyyatan Zamfara za su tashi daga jiharsu maimakon zuwa Sokoto ko Kano
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Ahmad Yusuf, kwararren edita ne a Legit Hausa da ya shafe tsawon shekaru yana kawo muku rahotannin siyasa, nishadi da al'amuran yau da kullum
Zamfara, Nigeria - Gwamna Dauda Lawal ya kafa tarihi a jihar Zamfara bayan tashin jirgin farko na maniyyata aikin Hajji daga Filin Jirgin Sama na Kasa da Kasa da ke Gusau.
Jirgin farko ya tashi ne daga Filin Jirgin Sama na Gusau ranar Juma’a, dauke da maniyyata 415 na jihar Zamfara cikin jirgin Max Air mai lamba NGL270 zuwa kasa mai tsarki.

Kara karanta wannan
Magana ta fito, an ji abin da Tinubu ya shirya yi a shekaru 2 na farko bayan ya ci zaben 2027

Source: Facebook
Gwamna Dauda Lawal ya kafa tarihi a Zamfara
Rahoton da jaridar Daily Trust ta wallafa yai Asabar, ya nuna cewa jirgin saman na kamfanin Max Air ya dauki maza 288 da mata 127, inda ya nufi kasar Saudiyya.
Yayin bikin kaddamar da fara jigilar maniyyata, Gwamna Lawal ya bayyana farin cikinsa da godiyarsa bisa ganin wannan babban ci gaba da ya zama tarihi a jihar Zamfara.
Gwamnan ya bayyana gina Filin Jirgin Sama na Kasa da Kasa a brinin Gusau a matsayin babban aikin da gwamnatinsa ta aiwatar wanda ya shiga tarihin jihar Zamfara.
Yadda Gwamnan Zamfara ya nuna farin ciki
“Ina matukar farin ciki yau da maniyyatanmu za su tashi kai tsaye daga Filin Jirgin Sama na Kasa da Kasa a Gusau zuwa kasar Saudiyya domin aikin Hajjin bana.
“Mutane da dama sun yi shakku cewa hakan ba zai taba zama gaskiya ba, amma yau ga shi ya tabbata. Mun fara aikin gina wannan filin jirgin sama a ranar 18 ga Yuni, 2024.
“Ba zan iya bayyana irin farin cikin da nake ciki ba. Dangane da maniyyatanmu, wannan babbar dama ce ta tafiya cikin sauki, cikin kasa da awa hudu za su isa Saudiyya. A baya, sai maniyyatanmu sun je Sokoto ko Kano kafin su samu jirgin zuwa Hajji.
- Gwamna Dauda Lawal.
Gwamna Lawal ya yi wa al'umma godiya
A rahoton Leadership, gwamnan ya nuna tsantsar farin cikinsa, inda ya ci gaba da cewa:
“Kalmomi ba za su iya bayyana cikakken farin cikina ba, amma zan ce wannan wani babban tarihi ne kuma cika alkawarin da muka dauka a lokacin yakin neman zabe. Ina da kudurin ci gaba da yi wa jiharmu ayyuka masu amfani.
“Ina gode wa al’umma bisa addu’o’insu da kuma amincewar da suka yi mana, wannan shi ne farkon babban alherin da ke tafe. Mun riga mun fara tattaunawa da kamfanonin jiragen sama da za su fara zirga-zirgar kasuwanci daga wannan fili.
"Ina yi wa maniyyatanmu fatan sauka tafiya da kuma aikin Hajji karbabbe. Haka kuma ina rokon su da su yi wa Zamfara da Najeriya addu’a.”

Source: Facebook
Mahajjatan Najeriya 54 na kwance a asibiti
A wani labarin, kun ji cewa hukumar NAHCON ta tabbatar da cewa mahajjata Najeriya 54 na kwance a asibitocin Saudiyya yayin da ake gudanar da aikin Hajjin 2026.
Shugaban tawagar likitocin Najeriya ne ya bayyana hakan yayin da yake yi wa manema labarai karin haske kan lafiyar mahajjatan Najeriya.
A cewarsa, tsananin zafi, gajiyar ibada da kuma wasu cututtuka da mahajjata ke dauke da su tun kafin tafiya na daga cikin abubuwan da suka haddasa matsalolin .
Asali: Legit.ng

