Kisan Buharin Daji: Yan bindiga sun cigaba da kai munanan hare hare a Zamfara
Tun bayan kisan shahararren dan fashin nan da ya addabi jihar Zamfara, Buharin Daji, yan bindiga sun kaddamar da wasu sabbin hare hare a kauyukan jihar Zamfara, kamar yadda Legit.ng ta gano.
Daily Trust ta ruwaito wasu yan bindiga sun kai hari a wani kauye mai suna Dogon Daji dake cikin karamar hukumar Maru, inda suka kashe mutane bakwai tare da satar yan mata guda biyu, ciki har da mai dauke da juna biyu.
KU KARANTA: Sabon tsari: Hukumar JAMB ta dauki nauyin makafi don zana jarabwar JAMB
Sanatan al’ummar, Sanata Kabiru Marafa ne ya tabbatar da wannan harin, inda yace gungun yan bindigan sun kai mutum 300 da suka dira kauyukan, inda suka tashi kauyukan gaba daya.
Marafa yace dukkaninsu dauke da bindiga kirar AK 47, sun dira kauykan ne da misalin karfe 4:30 na ranar Lahadi, inda suka kwashi tsawon lokaci suna tafka ta’asa iri iri, tare da aikata ma jama’an kauyukan aika aika daban daban.
Sai dai Sanatan ya tabbatar da zuwan Yansandan kauyukan, amma fa yace sai bayan da yan ta’addan suka tafi ne, sai ga Yansanda su taho mota mota, inda suka taimaka ma yan kauykan binne mutanen da aka kashe.
Ku biyo mu a https://www.facebook.com/naijcomhausa
ko a http://twitter.com/naijcomhausa
KU LATSA: Hanyar sauko da sabuwar manhajar jaridar Legit.ng Hausa cikin sauki
Ga masu shawara ko korafi, a same mu a labaranhausa@corp.legit.ng
Asali: Legit.ng