Wasu gagararrun yan fashi da makami guda 4 sun fada komar Yansandan jihar Kano
Runduna Yansandan jihar Kano ta sanar da kama wasu gungun yan fashi a makami na mutum hudu da suke tafka irin nasu ta’asar a tsakankanin jihar Jigawa da jihar Kano, ini rahoton kamfanin dillancin labaru.
Majiyar Legit.ng ta ruwaito shugaban wadannan gagararrun yan fashin, jami’in dansanda ne mai mukamin Sajan, Sajan Danjuma Sani, kuma an kama su ne bayan sun afka wani gidan baki mallakin mataimakin gwamnan jihar jigawa.
KU KARANTA: Wata sabuwar Annoba ta hallaka daliban sakandari guda 8 a jihar Katsina, an kulle makarantu
Kaakakin rundunar Yansanda, Magaji Musa Majia ne ya bayyana haka a lokacin da yake nuna ma yan jaridu yan fashin a ranar Talata 20 ga watan Maris, inda ya bayyana sunayen sauran; Nura Ahmed, Abdullahi Ahmed and Abubakar Uzairu.
“A ranar 18 ga watan Maris, da misalin karfe 9:30 na dare ne muka samu kira daga wani mutumi cewar fa yan fashi da makami suna sata, nan da kwamishinan Yansandan Rabiu Yusuf ya baiwa yansandan SARS umarnin fara bincike.
“Binciken ne ya tabbatar mana da cewar Danjuma tsohon Maigadi ne a gidan mataimakin gwamna jihar Jigawa, kuma shine ya tattaro sauran yan fashin guda uku domin su diran ma gidan.” Inji Majia.
Sai dai Kaakakin yace yan fashin na dauke ne da muggan makamai, a lokacin da suka far ma dansandan dake gadin gidan. Bugu da kari an kwato bindiga kirar AK 47 guda, alburusai, mota BMW ta naira miliyan 11, adda, wukake da tsabar kudi.
Daga karshe Kaakakin ya kammala jawabinsa da cewa yan fashin sun amsa laifukansu gaba daya, sa’annan nan gaba kadan za’a gurfanar dasu gana Kotu bayan kammala cikakken bincike game dasu.
Ku biyo mu a https://www.facebook.com/naijcomhausa
ko a http://twitter.com/naijcomhausa
Ga masu shawara ko korafi, a same mu a labaranhausa@corp.legit.ng
Asali: Legit.ng