Gwamna Nasir Ahmad El-Rufai kenan yana duba fitilun kan titi da aka saka a cikin garin Kaduna da kan sa
- Gwaman jihar Kaduna ya duba aikin sanya fitilu a cikin garin kaduna da kan sa a daren ranar Litinin
- Kamfanin Blue Camel Energy ta yi kwangilar saka fitilun kan titin cikin garin jihar Kaduna
A cikin daren ranar Litinin ne gwamnan jihar Kaduna, Mallam Nasir Ahmed El-Rufai, ya fita duba fitilun kan titi da ake sakawa a cikin garin jihar Kaudna da kan sa.
Mallam Nasiru El-Rufai, ya tsaya unguwar Ali Akilu Road dan duba fitilun da aka ba kamfanin Blue Camel Energy kwangilar sakawa.
Saka Fitilu a cikin garin jihar Kaduna yana cikin kudirin gwamnatin, Mallam Nasir El-Rufai na haskaka jihar a dan tabbatar da tsaro da kuma rage yin hatsari a cikin dare.
KU KARANTA : Yan bindiga a kauyukan jihar Zamfara sun hallaka mutane 8 basu ji ba, basu gani ba
Burin gwamnatin El-Rufai shine, dawo da martabar da kimar jihar Kaduna a fannoni daban-daban wanda ya hada da cigaban tattalin arziki, Ilimi, kiwon lafiya da kasuwanci.
Idan aka tuna baya a watan Fabrairu ne gwamnatin jihar Kaduna ta ce zata Za'a tallafawa malamai da gidaje da kuma karin albashi dan inganta fannin ilimi da ya tabarbarewa a jihar.
Idan ka na da wani shawara ko bukatan bamu labari, tuntube mu a labaranhausa@corp.legit.ng
Ku ci gaba da bin mu a
Facebook: https://www.facebook.com/naijcomhausa
Tuwita: http://twitter.com/naijcomhausa
KU LATSA: Sabuwar hanyar karanta labarain Legit.ng HAUSA https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en
Asali: Legit.ng