Wata sabuwar Annoba ta hallaka daliban sakandari guda 8 a jihar Katsina, an kulle makarantu

Wata sabuwar Annoba ta hallaka daliban sakandari guda 8 a jihar Katsina, an kulle makarantu

Wata Annoba ta kunno kai a jihar Katsina, inda ta shafi makarantun kwana na sakandarin Dutsanma, Kurfi da Kafur, wanda a yanzu haka tayi sanadin mutuwar dalibai guda 8, inji rahoton Daily Nigerian.

Wannan mummunan lamari yayi sanadiyyar kulle makarantun, wanda hakan ya sanya daliban makarantar komawa gidajensu, don gudun yaduwar cutar, kamar yadda majiyar Legit.ng ta ruwaito.

KU KARANTA: An hallaka mutane guda 3 a wani harin da yan bindiga suka kai jihar Kogi

Dan majalisa mai wakiltar mazabar Kurfi a majalsar dokokin jihar, Kabir Lawal ne ya sanar da haka a yayin zaman majalisar na ranar Litinin 19 ga watan Maris, inda ya bukaci a dauki matakin gaggawa don shawo kan lamarin.

A nasa bangaren, Kaakakin majalisar, Abubakar Kusada ya umarci kwamitin kula da kiwon lafiya na majalisar da ta gudanar da cikakken bincike game da annobar, sa’annan ta kawo ma majalisa rahotonta.

Hakazalika, suma yan majalisun dake wakiltar Kafur da Dutsanma, Garba Useini da Bishir Mamman, sun tabbatar da bullar wannan annoba, sai dai sun ce basu da alkalumman dake nuna adadin mutanen da annobar ta hallaka.

Ku biyo mu a https://www.facebook.com/naijcomhausa

ko a http://twitter.com/naijcomhausa

Ga masu shawara ko korafi, a same mu a labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Authors:
Mudathir Ishaq avatar

Mudathir Ishaq Mudathir Ishaq is the head of the Hausa desk at Legit.ng. He studied Industrial Chemistry as first degree at the University of Abuja, Journalism (CSR Specialization) with the Michigan State University and runs MSc Industrial Chemistry from the Nasarawa State University, Keffi. With more than a decade experience in news reporting and content editing, he has interviewed influential personalities. He can be reached on: mudathir.ishaq@corp.legit.ng