An Kama Dattijo da Ya Shiga Asibitin Funtua da Niyyar Satar Mahaifar Sabon Jariri
- Rundunar ‘yan sandan Katsina ta kama wani mutum da ake zargi da shiga asibitin Funtua domin neman mahaifar sabon jariri saboda tsafi
- Binciken ‘yan sanda ya nuna wanda ake zargin ya shiga harabar asibitin ne cikin yanayi mai tayar da hankali kafin a cafke shi
- Rundunar ta gargadi jama’a kan shiga kowane irin nau'i na ayyukan tsafi da laifuffukan da ke barazana ga cibiyoyin lafiya da rayuwar al’umma
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Sani Hamza, kwararren edita ne a fannin nishadi, al'amuran yau da kullum da kuma siyasa. Yana da shekaru sama da biyar a aikin jarida.
Katsina - Rundunar ‘yan sandan Jihar Katsina ta kama wani mutum bisa zargin yunkurin aikata laifi mai alaka da tsafi da ayyukan asiri a Babban Asibitin Funtua.
Rundunar ta bayyana cewa an kama mutumin ne bayan an gan shi yana yawo cikin yanayi mai tayar da hankali a harabar asibitin.

Source: Facebook
An kama wani mutum a asibitin Funtua
A wata sanarwa da jami’in hulda da jama’a na rundunar, DSP Abubakar Sadiq Aliyu, ya fitar, ya ce lamarin ya faru ne ranar 9 ga Mayun 2026 da misalin karfe 5:00 na yamma, in ji rahoton Punch.
Sanarwar ta ce shugaban jami’an tsaro na Babban Asibitin Funtua ne ya kai rahoto ga ‘yan sanda bayan daya daga cikin ma’aikatan asibitin ya lura da wani mutum da ba a san ko wanene ba yana yawo cikin asibitin cikin yanayi na rashin gaskiya.
Rundunar ta bayyana sunan wanda aka kama da Sagir Muntari, mai shekaru 50.
Yayin da ake yi masa tambayoyi, wanda ake zargin ya amsa cewa ya shiga asibitin ne domin neman mahaifar wani sabon jariri da nufin amfani da ita wajen tsafi da wasu ayyukan asiri.
Gargadin rundunar ‘yan sanda
‘Yan sanda sun ce bincike na ci gaba da gudana kafin gurfanar da shi a kotu bayan kammala bincike, kamar yadda rahoton ya nuna.
Rundunar ‘yan sandan Katsina ta gargadi jama’a kan shiga ayyukan tsafi da sauran laifuffuka masu barazana ga rayuka da cibiyoyin lafiya.
Ta kuma tabbatar da kudirinta na kare rayuka da dukiyoyin jama’a tare da tabbatar da tsaro a asibitoci da sauran wuraren gwamnati, kamar yadda rundunar ta wallafa a shafinta na Facebook.

Kara karanta wannan
Bayan tadiye yaransa a tantancewar APC, Fubara ya magantu kan alakarsa da jam'iyya

Source: Original
An bukaci jama’a su kai rahoto
‘Yan sanda sun bukaci al’umma su kasance masu lura tare da kai rahoton duk wani motsi ko hali da suke zargin ba daidai ba ne zuwa ofishin ‘yan sanda mafi kusa ko ta layukan gaggawa na rundunar.
Rundunar ta ce za ta ci gaba da sanar da jama’a duk wani sabon cigaba da aka samu game da binciken lamarin.
An cafke likita kan satar mahaifa
A wani labari, mun ruwaito cewa, dubun wasu ma'aikatan jinya ta cika yayin da aka cafke su da zargin batar da mahaifa da kuma cibiya bayan haihuwar jariri.
Rundunar 'yan sandan Kwara ta yi nasarar cafke likita da kuma masu taimaka masa guda hudu kan abin da ya faru a asibitin Iloffa da ke karamar hukumar Oke-Ero.
Wadanda ake zargin da ke amsa tambayoyi sun hada Dakta Ajibola da ma'aikatan jinya Rukayat Adeloye da Aishat Awolusi da Peace Alabi da Toyin Adewunmi.
Asali: Legit.ng
