An Raunana Karfin Turji, Ado Aliero bayan Cafke Mai ba Su Makamai a Katsina
- Sojojin rundunar Operation FANSAN YANMA sun kama wani da ake zargi da safarar makamai ga ’yan ta’adda a Katsina bayan samun sahihan bayanan sirri
- Rahotanni sun bayyana cewa wanda ake zargin yana kai wa fitattun shugabannin ’yan ta’adda irin su Bello Turji da Ado Aliero makamai
- Sojoji sun ce an cafke wanda ake zargin a Babban Asibitin Batsari yayin jinya, kuma ana ci gaba da bincike domin gano sauran masu safarar makamai
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Abdullahi Abubakar, Editan Legit Hausa ne ta bangaren siyasa, kasuwanci da al'amuran yau da kullum, ya na da gogewar aikin jarida sama da shekaru biyar.
Batsari, Katsina - Sojojin rundunar Operation FANSAN YANMA sun kama wani mutum da ake zargi da safarar makamai ga kungiyoyin ’yan ta’adda a Arewa maso Yamma.
Majiyoyin tsaro sun shaida cewa an kama wanda ake zargin mai suna Saidu Rabiu mai shekara 25 daga garin Wagini da ke karamar hukumar Batsari ta Katsina.

Kara karanta wannan
An kama dattijo da ya shiga asibitin Funtua da niyyar satar mahaifar sabon jariri

Source: Twitter
An kama mai safarar makamai a Katsina
Rahotanni daga Zagazola Makama sun ce an kama Saidu Rabiu ne ranar 15 ga Mayu, 2026 da misalin karfe 10:20 na safe bayan samun bayanan sirri masu inganci.
An bayyana cewa sojoji sun garzaya Babban Asibitin Batsari inda aka ce wanda ake zargin yana karbar magani saboda wata rashin lafiya da ba a bayyana ba.
Sojojin sun kama shi cikin lumana a asibitin ba tare da wata turjiya ba sannan suka tafi da shi domin gudanar da karin bincike.
Ana zargin Saidu na ba Turji, Aliero makamai
Binciken farko ya nuna cewa ana zargin Saidu Rabiu da kai wa fitattun shugabannin ’yan ta’adda makamai da alburusai masu inganci irin na sojoji.
Rahotanni sun ambaci Bello Turji da Ado Aliero cikin wadanda ake zargin suna hulda da wanda aka kama wajen samun makamai a yankin Arewa maso Yamma.
Sauran yan ta'addan da aka ambata sun hada da marigayi Kachalla Black da Yellow wadanda ake dangantawa da ayyukan ta’addanci a yankin.

Source: Original
Ana ci gaba da bincike kan Saidu Rabiu
Sojoji sun tabbatar da cewa wanda ake zargin yana tsare a hannunsu yayin da ake ci gaba da masa tambayoyi domin gano hanyoyin safarar makamai.
Hukumomin tsaro sun ce binciken zai taimaka wajen gano sauran mutane da kungiyoyin da ke tallafa wa ayyukan ’yan ta’adda da makamai a yankin Najeriya.
Al'ummar jihar Katsina da dama na yawan kiran hukumomi da su dauki matakan gaggawa domin kare rayukansu da dukiyoyinsu yayin da suke fuskantar hare-haren yan bindiga.
An kama dattijo da niyyar satar jariri
Mun ba ku labarin cewa rundunar ‘yan sandan Katsina ta kama wani mutum da ake zargi da shiga asibitin Funtua domin neman mahaifar sabon jariri saboda tsafi.
Binciken ‘yan sanda ya nuna wanda ake zargin ya shiga harabar asibitin ne cikin yanayi mai tayar da hankali kafin a cafke shi wanda hakan ya jawo hankulan mutane.
Rundunar ta gargadi jama’a kan shiga kowane irin nau'i na ayyukan tsafi da laifuffukan da ke barazana ga cibiyoyin lafiya da rayuwar al’umma baki daya.
Asali: Legit.ng
