Majalisar jihar Kano zata dakatar da biyan fansho ga tsofin gwamnoni da mataimakansu

Majalisar jihar Kano zata dakatar da biyan fansho ga tsofin gwamnoni da mataimakansu

- Idan kudurin ya tabbata, za a dakatar da fanshon tsofin gwamnoni da mataimakansu dake rike da mukaman siyasa

- Yanzu kudirin na gaban kwamitin wucin gadi na majalisar jihar

- A ranar 27 ga watan Fabrairu ne jihar Kwara ta zartar da kudirin daina biyan tsofin gwamnonin jihar fansho da wasu alwus

A jiya, Litinin, 19 ga watan Maris, majalisar jihar Kano ta fara tattauna kudirin bukatar yin kwaskwarima ga dokar tsofin gwamnoni da mataimakansu a jihar kudaden fansho da garatuti.

Majalisar ta ce yiwa dokar gyara zai ragewa gwamnati kashe kudaden gudanarwa.

Kamfanin dillancin labarai na kasa (NAN) ya rawaito cewar, mamba a majalisar, Labaran Madari; mai wakiltar karamar hukumar Warawa, ya gabatar da kudirin gaban majalisar.

Majalisar jihar Kano zata dakatar da biyan fansho ga tsofin gwamnoni da mataimakansu
Zauren majalisar jihar Kano

Madari ya shaidawa 'yan majalisar cewar yin gyara ga dokar zai ragewa gwamnati kashe kudi a bangaren gudanarwa BV tare da bayyana cewar da ma bai dace ake biyan tsohon gwamna ko mataimakin gwamna ba yayin da yake rike da wani mukamin siyasa ba.

DUBA WANNAN: Jonathan ya harzuka, ya kira Osinbajo makaryaci

Madari ya bukaci a dakatar da biyan duk wani tsohon gwamnan jihar ko mataimakin gwamna dake rike da wani mukamin siyasa har sai bayan ya sauka daga mukamin da yake kai.

Wannan kudiri na zuwa ne makonni kadan bayan majalisar jihar Kwara ta zartar da dokar dakatar da biyan tsofin gwamnonin jihar da mataimakansu kudin fansho yayin da su ke rike da wani mukamin.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/naijcomhausa

Twitter: https://twitter.com/naijcomhausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Authors:
Mudathir Ishaq avatar

Mudathir Ishaq Mudathir Ishaq is the head of the Hausa desk at Legit.ng. He studied Industrial Chemistry as first degree at the University of Abuja, Journalism (CSR Specialization) with the Michigan State University and runs MSc Industrial Chemistry from the Nasarawa State University, Keffi. With more than a decade experience in news reporting and content editing, he has interviewed influential personalities. He can be reached on: mudathir.ishaq@corp.legit.ng