Tsohon shugaban kasa Cif Olusegun Obansanjo ya karbi takardar shaidar kammala digirin digirgir
- Obansanjo ya karbi takardar shaidar kammala digirin digirgir
- Ferfesa Abdalla Uba Adamu ya ceObasanjo dalibi ne mai bin doka da oda
Tsohon shugaban kasar Najeriya, Cif Olusegun Obasanjo, ya karbi takardar shaidar kammala karatun digirin digirgir a budaddiyar jami'ar kasar ta National Open University.
Daya daga cikin mallaman jami’an, Ferfesa Abdalla Uba Adamu, ya ce, Cif Olusegun Obasanjo ya kasance dalibi mai bin dokokin da ka’idojin jami’ar Kaman yadda sauran daliban suke yi.
Mista Obasanjo ya kasance daya daga cikin dalibai sama da 14,000 da aka yaye daga jami'ar kasa ta National Open University.
Obasanjo ya karbi shaidar kammala digirin dokta a fannin addinin Kirista (Christian Theology).
KU KARANTA : Babban malamin addini ya shiga takarar tikitin zama gwamna a Najeriya
Farfesa Abdalla Uba Adamu, ya ce, Oabsanjo, bai taba fashin yin aikin gida wato 'assignment' da ake badawa a makarnata ba.
Sannan Obasanjo ya bukaci mallaman makaranatar kada su nuna masa fifiko fiye da sauran daliban saboda girman sa.
Idan ka na da wata shawara ko bukatar ba mu labari, a tuntube mu a labaranhausa@corp.legit.ng
Ku same mu a https://www.facebook.com/naijcomhausa
Ko a http://twitter.com/naijcomhausa
Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en
Asali: Legit.ng