Wasu jihohi a yankin arewa suna fuskantar barazanar yunwa

Wasu jihohi a yankin arewa suna fuskantar barazanar yunwa

- Matsalar yunwa dai ba karamar barazana ba ce a duniya musamman ma a yankin Afurka, inda zaka iske mutum yana cin abinci sau daya a rana wani ma baya samun dayan sai da kameme. A yanzu haka dai matsalar tana neman shafar yankin Arewa na Najeriya.

- Hukumomin abinci dana bunkasa aikin gona tare da hadin guiwar hukumar bada agajin gaggawa na majalisar dinkin duniya sun yi hasashen cewa akwai barazanar yunwa akan jihohi sama da 16 a yankin arewacin Najeriya.

Wasu jihohi a yankin arewa suna fuskantar barazanar yunwa
Wasu jihohi a yankin arewa suna fuskantar barazanar yunwa

Hadakar manyan Hukumomin Abinci na Duniya sunyi gargadi akan yiwuwar samun karancin abinci mai tsanani da zata shafi kusan kimanin mutane miliyan hudu dake jihohi 16 na yankin Arewacin Najeriya.

DUBA WANNAN: Buhari ya gargadi direbobin manyan motoci dasu guji ajiye motoci akan babban titi

Hukumar abinci da bunkasa aikin gona da take karkashin majalisar dinkin duniya (FAO), da hadin gwiwar hukumar bayar da agajin abinci ta majalisar dinkin duniya (WFP), hukumomin sunce da alamun matsalar ba wai iya jihohin zata shafa ba hatta birnin tarayya matsalar zata je can, mutukar ba a dauki matakai na gaggawa ba akan matsalar.

Hukumomin WFP da FAO sun kawo jerin jadawalin jihohin da karancin abincin zai shafa, jihohin sun hada da jihar Adamawa, Bauchi, Benuwe, Borno, Gombe, Filato, Jigawa, Kano, Kaduna, Katsina, Kebbi, Niger, Sokoto, Taraba, Yobe, Zamfara.

Latsa wannan domin samun labarai a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/naijcomhausa

Twitter: https://twitter.com/naijcomhausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Authors:
Mudathir Ishaq avatar

Mudathir Ishaq Mudathir Ishaq is the head of the Hausa desk at Legit.ng. He studied Industrial Chemistry as first degree at the University of Abuja, Journalism (CSR Specialization) with the Michigan State University and runs MSc Industrial Chemistry from the Nasarawa State University, Keffi. With more than a decade experience in news reporting and content editing, he has interviewed influential personalities. He can be reached on: mudathir.ishaq@corp.legit.ng