Kungiyar kare hakkin dan Adam na Amnesty	 ta zargi sojin Najeriya akan sace 'yan matan Dapchi

Kungiyar kare hakkin dan Adam na Amnesty ta zargi sojin Najeriya akan sace 'yan matan Dapchi

- Kungiyar Amnesty ta ce rundunar sojin Najeriya tana da masaniya akan harin Dapchi

- Shugabannin yannkin Dapchi sun sanar da sojoji isowar garin amma basu yi komai inji Kungiyar Amensty

Kungiyar kare hakkin dan Adam na Amnesty International, ta ce sojojin Najeriya sun yi kunnen uwar shegu akan gargadin da aka musu na cewa Boko haram za su kowa wa yankin Dapchi hari sa'o'i kalilan gabannin a sace 'yan matan GSS Dapchi sama da guda 100.

Wata guda kenan da mayakan Boko Haram suka sace 'yan matan a lokacin da suke makaranta a garin Dapchi na jihar Yobe.

Kungiyar kare hakkin dan Adam na Amnesty	 ta zargi sojin Najeriya akan sace 'yan matan Dapchi
Kungiyar kare hakkin dan Adam na Amnesty ta zargi sojin Najeriya akan sace 'yan matan Dapchi

Kungiyar Amnesty ta kara dacewa shugabannin yankin, sun sanar da sojoji labarin tawagar motocin mayakan kungiyar Boko Haram da aka gani a wani kauye mai nisan kilomita 30 daga garin Dapchi, kwana guda kafin aka sace ‘yan matan.

KU KARANTA : Hukumar DSS ta bayana yadda ta kama wani shahararren mai safarar makamai a Najeriya

Sunce ko lokacin da mayakan Boko Haram suka iso yankin sai da aka sanar da sojoji, amma basu wani abu a kai ba.

Mai magana da yawun bakin rundunar Sojin Najeriya, yace gwamnatin ta kafa kwamitin bincike akan akan gaxawar jami’an tsaro a yankin.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/naijcomhausa

Twitter: https://twitter.com/naijcomhausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari, Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Authors:
Mudathir Ishaq avatar

Mudathir Ishaq Mudathir Ishaq is the head of the Hausa desk at Legit.ng. He studied Industrial Chemistry as first degree at the University of Abuja, Journalism (CSR Specialization) with the Michigan State University and runs MSc Industrial Chemistry from the Nasarawa State University, Keffi. With more than a decade experience in news reporting and content editing, he has interviewed influential personalities. He can be reached on: mudathir.ishaq@corp.legit.ng