Shugaban kasar Koriya ta Arewa ya sake razana Turai
Rahotanni sun kawo cewa hukumar leken asirin kasar Jamus ta bayyana wani sabon al’amari akan nukiliyar kasar Koriya ta Arewa wanda ya kuma razana kasashen Turai.
Bisa rahotanni daga daya daga cikin jaridun na Jamus wato Bild, a lokacin wata ganawar sirri da ya gudanar tare da yan majalisar dokoki na kasarsa, shugaban BND Ole Diehl, ya bada tabbacin cewa makaman Koriya ta Arewa na iya cimma kasashen Turai a cikin kiftar ido.
'Yan majalisar dokokin Jamus, wadanda labarin ya razana su ne suka fallasa wannan sirrin har 'yan jarida n Bild suka ji.
An tabbatar da cewa makaman Koriya ta Arewa na iya zuwa daga wata nahiya ya zuwa wani bangaren duniya cikin kankanen lokaci.
A baya Legit.ng ta rahoto cewa tsohon shugaban kasar Faransawa Nicolas Sarkozy na tsare sakamako bincike da ake kan cewa ya karbi miliyoyin kudaden euro ba bisa doka ba daga marigayi Moammar Gadhafi.
KU KARANTA KUMA: 2019: Gwamnoni da sanatoci masu yiwa Buhari biyayya na shirin juya ma Saraki baya
Wata majiya ta bayyana cewa Sarkozy na tsare a hannun yan sanda a ofishin yan sanda dake Nanterre, kudancin kasar Faris. Mutumin yayi magana ne bisa sharadin sirrinta sunansa saboda baa bashi umurnin tattauna al’amarin ga al’umma ba.
Idan ka na da wata shawara ko bukatar ba mu labari, a tuntube mu a labaranhausa@corp.legit.ng
Ku same mu a https://www.facebook.com/naijcomhausa
Ko a http://twitter.com/naijcomhausa
Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en
Asali: Legit.ng