Buhari ya gargadi direbobin manyan motoci dasu guji ajiye motoci akan babban titi

Buhari ya gargadi direbobin manyan motoci dasu guji ajiye motoci akan babban titi

- Shugaba kasa Muhammadu Buhari yayi gargadi ga direbobin manyan motoci dana tankokin mai dasu guji ajiye motocin su akan babban titi, saboda hakan yana kawo cunkoso akan manyan titunan kasar nan, sannan ya roke kungiyoyin direbobin dasu gina wuraren ajiye motocin saboda rage cunkoson akan titunan

Buhari ya gargadi direbobin manyan motoci dasu guji ajiye motoci akan babban titi
Buhari ya gargadi direbobin manyan motoci dasu guji ajiye motoci akan babban titi

Shugaban kasa Muhammadu Buhari ya gargadi direbobin manyan motoci dasu guji ajiye motoci a kan manyan titi, sannan kuma su gina wuraren ajiye motocin domin kawo saukin zirga-zirga akan manyan titi, da kuma rage cinkoson motoci a kasar nan.

DUBA WANNAN: Trump ya nemi tallafin kudi a wurin kasar Saudiyya

Shugaban kasar yayi gargadin ne a lokacin da ya halarci wani taro wanda ma'aikatar wutar lantarki, da ayyuka ta tarayya ta shirya jiya a Abuja.

Hukumar ta shirya taron ne domin ta bayyana wa al'umma irin cigaban da aka samu wurin gyaran hanyoyin gwamnatin tarayya. Sannan Shugaba Buhari ya ce, hakan wani yunkuri ne da hukumar take na kawo cigaba ga al'umma ta hanyar gyaran manyan titi na gwamnatin tarayya, inda a yanzu haka aikin ya garu daga kaso 15 zuwa 30. Sannan kuma ya bayyana muhimmancin hanyoyi masu kyau da kuma irin cigaban da zasu kawo wa Najeriya.

A cewar shi: "Kawar da matsalar obalodi da manyan motoci suke yi zai kawo cigaba ta bangaren kasuwanci, sannan kuma zai rage yawan kudin da gwamnati take karba akan manyan motoci. Ina roqar dukkan direbobin manyan motoci dana tankar mai da su daina ajiye motoci akan manyan titi musamman ma titi na gwamnatin tarayya, saboda hakan yana kawo cunkoson abubuwan hawa.

"Manyan titunan su zamo babu cunkoso a koda yaushe, saboda hakan zai taimaka wurin kiyaye hadura na ababen hawa. Sannan kuma masu motocin su gina wuraren ajiye motocin a duk wurin da suka ga ya dace.

Shugaban kasar ya bayyana cewa gwamnatin tarayya tana kokari wurin ganin ta rage cunkoson ababen hawa ta hanyar gina hanyoyin jirgin kasa, domin kawo saukin zirga - zirga ga al'umma.

Latsa wannan domin samun labarai a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/naijcomhausa

Twitter: https://twitter.com/naijcomhausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Authors:
Mudathir Ishaq avatar

Mudathir Ishaq Mudathir Ishaq is the head of the Hausa desk at Legit.ng. He studied Industrial Chemistry as first degree at the University of Abuja, Journalism (CSR Specialization) with the Michigan State University and runs MSc Industrial Chemistry from the Nasarawa State University, Keffi. With more than a decade experience in news reporting and content editing, he has interviewed influential personalities. He can be reached on: mudathir.ishaq@corp.legit.ng