Ko sama ko kasa: An nemi shaida an rasa a wajen sauraran karar Maryam Sanda
Rahotanni sun kawo cewa babban kotun tarayya dake sauraron shari’an Maryam Sanda matar da aka zarga da kashe mijinta ta daga sauraron karar sakamakon rashin bayyanan shaida wanda zai amsa tambayoyi a kotun.
A ranar Litinin, 19 ga watan Maris ne aka dawo zaman kotu bayan an bayar da belin Maryam Sanda, inda daga baya lauyaan wacce ake zargi ya sanarwa da mai shari’a cewa babban shaida da ya kamata a fara yiwa tambayoyi bai bayyana a kotu ba.
Lauyan wacce ake tuhuma kan laifin kisan James Idachaba ya shaida ma kotu cewa ya halarci dakin tare da shaidu su hudu sai dai daga bisani an nemi daya daga cikin su an rasa.
Sauran shaidun da aka gabatar a kotun sun hada da Maimuna Sanda (mahaifiyar Maryam), Aliyu Sanda (Dan uwan ta) da kuma Sadiya Aliyu (Yar aikin gida).
Ana zargin su da sa hannu wajen kashe marigayi Bilyaminu.
KU KARANTA KUMA: Shugaban kasar Koriya ta Arewa ya sake razana Turai
Mai shari'a Halilu Yusuf ya daga ranar saurara karar zuwa ranar 19 da 20 ga watan Afrilu.
Sai dai alkali mai bada kariya Joseph Daudu ya nemi kotu da ta yi watsi da bukatar da lauyan maryam ya nema a laifin kisa da aka shigar.
A ranar 7 ga watan Maris, kotun ta ba da belin wacce ake zargin bayan sun bukaci haka a karo na biyar.
Mai shari’a Yusuf Halilu, wanda yaki amincewa da bayar da belinta har sau hudu, ya bayyana cewa kotun ta gamsu da dalilin rashin lafiya da aka gabatar akan Maryam.
Idan ka na da wata shawara ko bukatar ba mu labari, a tuntube mu a labaranhausa@corp.legit.ng
Ku same mu a https://www.facebook.com/naijcomhausa
Ko a http://twitter.com/naijcomhausa
Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en
Asali: Legit.ng