Jerin Masu Neman Takarar Majalisar Tarayya da APC Ta Yi Watsi da Su a Wurin Tantancewa
Jam’iyyar APC ta fitar da jerin sunayen masu neman takarar kujerar Majalisar Wakilai da ta sanya wa alamar “ba a amince da su ba” a jihohi da dama a Najeriya.
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Ahmad Yusuf, kwararren edita ne a Legit Hausa da ya shafe tsawon shekaru yana kawo muku rahotannin siyasa, nishadi da al'amuran yau da kullum
Daga cikin jihohin da masu neman takara suka gaza tsallake matakin tantance wa a APC akwai Ondo, Bauchi, Ebonyi, Kogi da Rivers.

Source: Twitter
Yadda APC ta gudanar da tantancewa
Sunayen na kunshe ne a cikin wata sanarwa da APC ta wallafa a shafinta na X mai dauke da sa hannun sakataren yada labaran jam'iyya na kasa, Felix Morka.
Jam'iyyar APC ta bayyana cewa sunayen na daga cikin wadanda ba su tsallake tsarin tantancewar da jam’iyyar ta gudanar domin tabbatar da cancantar su ba a mazabu daban-daban.
Sanarwar ta ce:
“Kwamitocin tantance ‘yan takara na jam’iyyar APC ne suka gudanar da aikin bisa tsarin da dokokin jam’iyyar suka tanada.”
Masu neman takarar APC ta soke
Sunayen masu neman takara da ba su cancanta ba, wadanda jam'iyyar APC ta fitar yau Asabar, 16 ga watan Mayu, 2026, sun hada da;
Jihar Ondo
1. Hon. Adefisoye Tajudeen (Idanre/Ifedore)
2. Olusegun Victor Ategbole (Akoko South-East/South-West)
3. Seun Oluwashina Ajongbolo (Akoko South-East/South-West)
4. Rt. Hon. Arowole Ayodeji Samuel (Owo/Ose)
5. Morufu Tosin Ibrahim (Akoko North-East/North-West)
6. Oseni Oyeniyi (Akoko North-East/North-West)
7. Olaleye John Adedipe (Akoko North-East/North-West)
Jihar Bauchi
8. Dr. Bashir Ibrahim Bello (Mazabar Darazo/Ganjuwa)
Jihar Ebonyi
9. Hon. Idu Igariwe (Mazabar Afikpo/Edda)
Jihar Kogi
10. Sanni Salau Ogembe (Mazabar Okene/Ogori-Magongo)
Jihar Rivers
11. Air Commodore John Azubuike Opara (mai ritaya) – Mazabar Port Harcourt
12. Hon. Anderson Allison Igbiki – Mazabar Okrika/Ogu-Bolo
13. Awaji Imombek D. Abirite – Mazabar Andoni/Opobo-Nkoro
14. Hon. Boma Goodhead – Mazabar Asari-Toru/Akuku-Toru
APC ba ta bayyana cikakken dalilin da ya sa aka sanya wa wadannan masu neman takara alamar “ba a amince su yi takara ba.”
Yadda aka gudanar da zabuka a jihohi
A wani bangare kuma, a jihar Katsina, Jamila Abdu Mani, mai taimaka wa Gwamna Dikko Radda kan harkokin ilimin yara mata, ta lashe zaben fidda gwani na APC na mazabar Mani/Bindawa ta tarayya.
Haka kuma a jihar Adamawa, an samu cikas wajen gudanar da zabukan fitar da gwani na kato bayan kato na Majalisar Wakilai a wasu gundumomi sakamakon rashin isowar jami’an da za su gudanar da zaben.

Source: Getty Images
Mambobin jam’iyyar APC a Girei, Yola North da Yola South sun shafe sa’o’i suna jira ba tare da samun wani bayani kan fara zaben ba.
Zabukan fitar gwanin APC na daga cikin shirye-shiryen da jam’iyyar le yi domin tunkarar babban zaben 2027.
Jam'iyyu 22 sun cika sharadin INEC
A wani labarin, kun ji cewa hukumar INEC ta tabbatar da cewa jam'iyyun siyasa 22 sun mika kundin rijistar mambobinsu kamar yadda dokar zabe ta 2026 ta tanada.
INEC ta ce mika kundin rajistar ya biyo bayan karin wa’adin da ta bai wa jam’iyyun siyasa bayan da suka nuna damuwa kan wa’adin farko.
A cewar hukumar, dukkan jam’iyyun siyasar sun mika kundin rajistar mambobinsu a ranar 8 ga Mayu, 2026 ko kafin hakan, kwanaki biyu kafin cikar sabon wa’adin ranar 10 ga Mayu.
Asali: Legit.ng


