An hallaka mutane guda 3 a wani harin da yan bindiga suka kai jihar Kogi
Rundunar Yansandan jihar Kogi ta tabbatar da mutuwar mutane guda uku a sakamakon wani harin ba sani ba sabo da yan bingida suka a kauyen Agbenema dake karamar hukumar Omala na jihar Kogi.
Kamfanin dillancin labarun, NAN, ta ruwaito Kaakakin rundunar Yansandan jihar, ASP Willaim Aya ya sanar da haka, inda yace an kai wannan harin ne a ranar 19 ga watan Maris.
KU KARANTA: Kisan Buharin Daji: Yan bindiga sun cigaba da kai munanan hare hare a Zamfara
Sai dai majiyar Legit.ng ta ruwaito Kaakaki Aya ya musanta labarin da ake yadawa na cewa mutane 11 ne suka rasa rayukansu, har ma ana cewa wai har da wani basaraken gargajiya a cikin wadanda aka kashe.
Mista Aya yace kwamishinan Yansandan jihar, Ali Janga ya bukaci jama’a da su cigaba da gudanar da al’amuransu na yau da kullum, ba tare da wata fargaba ba.
Hakazalika kwamishina ya shawarci masu amfani da shafukan sadarwa na yanar gizo da su dinga tabbatar da sahihancin labarai kafin su wallafa a shafukan nasu, don gudun kada su dinga shayar da mutane labaran karya.
Ku biyo mu a https://www.facebook.com/naijcomhausa
ko a http://twitter.com/naijcomhausa
KU LATSA: Hanyar sauko da sabuwar manhajar jaridar Legit.ng Hausa cikin sauki
Ga masu shawara ko korafi, a same mu a labaranhausa@corp.legit.ng
Asali: Legit.ng