Jerin Manyan mata masu kudin Duniya a 2018

Jerin Manyan mata masu kudin Duniya a 2018

Idan kana maganar masu kudin Duniya dole sai dai ka fara kiran irin suBill Gates, Jebb Bezos da sauran su. Sai dai duk da haka a sahun Attajirai akwai wasu tsirararun mata wanda su ka gada da wanda su ka nema. Wadannan mata sun hada da:

1. Alice Walton

A matan Duniya babu mai kudin Alice Walton wanda ta mallaki abin da yah aura Dala Biliyan 46 yanzu a Duniya. Alice ita kadai ce diyar mai kamfanin Walmart watau Sam Walton.

Jerin Manyan mata masu kudin Duniya a 2018
Alice Walton ce wanda ta fi kowa arziki a matan Duniya

2. Francoise Bettencourt Meyers

Bayan Walton wanda ita ce ta 16 a masu kudin Duniya akwai kuma Meyers wanda ta ba Dala Biliyan 42 baya. Ita kuma Francoise Bettencourt tayi fice ne wajen kayan shafa.

Jerin Manyan mata masu kudin Duniya a 2018
Liliane Bettencourt tana cikin manyan masu kudin Duniya kafin ta rasu

KU KARANTA: Shugaban Koriya ya kuma tada hankalin kasashen Turai

3. Maria Franca Fissolo

Mujallar Forbes ta balayyana cewa Bazawarar Michele Ferroro ce ta 3 a mata masu kudin Duniya. Ferroro ta mallaki abin da yah aura Dala Biliyan 32 ta hanyar alewar ta na Nutella.

Bayan nan kuma akwai irin su Jacqueline Mars, Zhou Qunfei, da Sherry Brydson ta kasar Kanada wanda su ka Biliyoyin kudi baya.

Idan ka na da wata shawara ko bukatar ba mu labari, a tuntube mu a labaranhausa@corp.legit.ng

Ku same mu a https://www.facebook.com/naijcomhausa

Ko a http://twitter.com/naijcomhausa

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Asali: Legit.ng

Authors:
Muhammad Malumfashi avatar

Muhammad Malumfashi (Hausa writer) M. Malumfashi ya samu Digirin farko a ilmin komfuta a ABU Zaria. Baya ga haka ya yi Digirgir a fannin kula da bayanai da wani Digirgir a ilmin aikin jarida duk daga jami'ar. Malumfashi ya kan kawo labaran siyasa, addini, wasanni da al’ada. Ya halarci taron karawa juna sani iri-iri. Imel: muhammad.malumfashi@corp.legit.ng