Latest
Shahararriyar jarumar nan da tayi fice a harkar shirya fina-finan Hausa Maryam Both tayi raddi ga masu amfani da sunanta a shafukan yanar gizo. Jarumar tayi Allah ya isa ga masu amfani da sunan nata suna bata mata suna.
Isah ya bayyana ma majiyar NAIJ.com cewa ya bar matarsa da ciki, don kwatakwata watanni shidda kenan da aurensu, amma yace daga bisani ya samu labarin ta haihu a hannu yan Boko Haram, inda suka rada ma yaron nasa suna Muhammad.
Wata sabuwa inji yan caca, wasu miyagu masu garkuwa da mutane dauke da muggan makamai sun yi shigar burtu, inda suka sanya kayan mata, suka afka cikin wani gida, suka yi awon gaba da wasu iyaye mata guda biyu a jihar Katsina.
Za ku ga harsashen da NAIJ Hausa su kayi na wasu ‘Yan siyasar kasar nan da mu ke tunanin Wazirin Adamawa Atiku zai iya zaba a domin su yi takarar Mataimakin Shugaban kasa a zabe mai zuwa na 2019 karkashin Jam’iyyar PDP.
Sai dai yace tun cikin na dna wata uku ne ya bukaci ta zubar da cikin, amma ta ki, inda bayan watanni hudu, ya kara mika mata bukatarsa na zubar da cikin, nan tace atabau, daga nan ne ya yanke shawarar kasheta tunda dai ya fahimci
A kwanakin baya ne dai majalisar koli ta jam’iyyar APC ta dauki matakin kara ma shuwagabannin jam’iyyar APC wa’adin mulki na tsawon shekara guda daya, tun daga mazabu har zuwa matakin kasa gaba daya, sai dai matakin bai dace tsari
Za ku ji cewa an yi nisa kwarai da gaske a wani aiki da ake ta faman yi na titin kasa a Unguwar Kofar Ruwa a cikin karamar Hukumar Dala Garin Kano. Wannan yana cikin ayyukan da Gwamna Kwankwaso ya fara a lokacin sa.
Za ku ji cewa 'Yan Majalisa sun gano wata badakalar da aka tafka a CBN. Majalisar Wakilan Tarayya ta ba Gwamnan CBN kwana biyu yayi bayanin abin da ya auku. Yanzu haka Majalisa ta ba Godwin Emefiele kwana 2 ya hallara gaban ta.
Daya daga cikin 'yan majalisar wakillai a Najeriya mai suna Honourable Julius Pondi ya yayata rabawa al'ummar da yake wakilta garin kwaki a matsayin kyauta a gare su. Ganau dai sun shaidawa majiyar mu cewa garin kwakin da dan maja
Masu zafi
Samu kari