Dan majalisar tarayya a Najeriya ya rabawa al'ummar sa garin kwaki

Dan majalisar tarayya a Najeriya ya rabawa al'ummar sa garin kwaki

- Wani dan majalisar wakillan Najeriya ya yayata ba al'ummar sa garin kwaki

- Dan majalisar sunan sa Honourable Julius Pondi

- Honourable Julius Pondi yana wakiltar mazabar Burutu a majalisar

Daya daga cikin 'yan majalisar wakillai a Najeriya mai suna Honourable Julius Pondi ya yayata rabawa al'ummar da yake wakilta garin kwaki a matsayin kyauta a gare su.

Dan majalisar tarayya a Najeriya ya rabawa al'ummar sa garin kwaki
Dan majalisar tarayya a Najeriya ya rabawa al'ummar sa garin kwaki

KU KARANTA: PDP na zawarcin Sanata Shehu Sani

Ganau dai sun shaidawa majiyar mu cewa garin kwakin da dan majalisar ya raba bai da wani yawan da har ya kai a yayata shi a kafar sadarwar zamani domin kuwa bai ma kai na Naira 200 ba a kasuwa.

A wani labarin kuma, Rahotannin da muke samu daga majiyoyin mu da dama na nuni ne da cewa jam'iyyar adawa ta Peoples Democratic Party, PDP a takaice na cigaba da zawarcin Sanata Shehu Sani da ke wakiltar mazabar jihar Kaduna ta tsakiya ya dawo cikin ta.

Mun samu kuma dai cewa Sanatan na ta fuskantar matsin lamba daga bangarori da dama kuma mabanbanta da suka hada da kungiyoyin matasa da ma dattijai daga jam'iyyar ta PDP.

Idan ka na da wani shawara ko bukatan bamu labari, tuntube mu a labaranhausa@corp.legit.ng Ku ci gaba da bin mu a Facebook: https://www.facebook.com/naijcomhausa da

Kuma Tuwita: http://twitter.com/naijcomhausa

KU LATSA: Sabuwar hanyar karanta labarain Legit.ng HAUSA

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Asali: Legit.ng

Authors:
Mudathir Ishaq avatar

Mudathir Ishaq Mudathir Ishaq is the head of the Hausa desk at Legit.ng. He studied Industrial Chemistry as first degree at the University of Abuja, Journalism (CSR Specialization) with the Michigan State University and runs MSc Industrial Chemistry from the Nasarawa State University, Keffi. With more than a decade experience in news reporting and content editing, he has interviewed influential personalities. He can be reached on: mudathir.ishaq@corp.legit.ng