Majalisa ta taso Gwamnan babban bankin Najeriya Godwin Emefiele a gaba
- 'Yan Majalisa sun gano cewa CBN ta zari wasu kudi daga asusun TSA
- Ministar kudin da Akantan kasar ba su da masaniya kan abin da ya faru
- An ba Emefiele kwana 2 yayi wa Majalisa bayanin yadda aka zari kudin
Mun samu labari jiya daga Jaridar Daily Trust cewa 'Yan Majalisar sun gano wata badakalar da aka tafka ta assun bai-daya watau TSA Gwamnatin Shugaba Buhari inda ta nemi Gwananan babban banki CBN yayi mata bayani.
Majalisar kasar ta aikawa Gwamnan Babban bankin Najeriya sammaci a dalilin zargin da ake yi na cire wasu makudan kudi daga asusun TSA da aka yi aka maidawa wasu Hukumomin kasar ba da amincewar Majalisar kasar ba kwanaki.
KU KARANTA: Majalisa ta jinkirta lokacin da za a amince da kasafin kudin bana
Honarabul Abubakar Nuhu Danburam shi ne 'Dan Majalisar da ya gudanar da bincike inda ya gano cewa CBN ta zari wasu kudi ba ta inda ya dace ba ta ba wata Hukuma. Ministar kudin kasar da sauran manyan ba su ma san anyi ba.
Akanta Janar na kasar Idris Ahmed wanda ya wakilci Ministar kudi Kemi Adeosun a wani zama yace da labarin wanna abu da CBN tayi don haka aka nemi Gwamnan bankin yayi wa Majalisa bayanin duk abin da ya faru cikin kwanaki biyu.
Idan ka na da wata shawara ko bukatar ba mu labari, a tuntube mu a labaranhausa@corp.legit.ng
Ku same mu a https://www.facebook.com/naijcomhausa
Ko a http://twitter.com/naijcomhausa
Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en
Asali: Legit.ng