Sojin Saman Najeriya sun fara aikin duba marasa lafiya na kwanki 3 a sansanin 'yan gudun hijira na Benuwai
Hukumar Sojin Saman Najeriya ta kaddamar da aikin duba marasa lafiya kyauta a sansanin yan gudun hijira na Abagana-Agan da ke jihar Benuwai.
Aikin duba marasa lafiyan da za'ayi na kwanaki uku da ya hada da tiyatan idanu, samar da gilashin ido, bayar da maganin tsutsan ciki da kuma rabar da ragar sauro da sauran gwaje-gwajen duba marasa lafiya.
A wajen kaddamar da aikin, Gwamna Samuel Ortom na jihar Benuwai ta bakin kwamishina lafiya na jihar Dr. Cecilia Ojabo ya mika godiyarsa ga Hukumar Sojin saman inda yace wannan taimakon zai rage radaddin wahalar da yan gudun hijirar ke fama dashi.
KU KARANTA: Hukumar kwastam ta kama buhunan shinkafa 589 a cikin motar dakon man fetur
Umurnin gudanar da wannan aikin ya fito ne daga bakin shugaban hafsin sojin na sama, Air Marshal sadique Abubabakar.
Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en
Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:
Facebook: https://facebook.com/naijcomhausa
Twitter: https://twitter.com/naijcomhausa
Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,
Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng
Asali: Legit.ng