Na shiga kungiyar asiri ne don cinma burina na zama dan siyasa

Na shiga kungiyar asiri ne don cinma burina na zama dan siyasa

- Hukumar ‘Yan Sanda ta kama shugaban wata kungiyar asiri a jihar Abia

- Wanda ake zargin, Princewill Okechukwu dalibi ne dan 400L a jami’ar jihar Abia da ke Uturu

- Yace makiyansa ne, dake da bukatar matsayinsa, suka kai kararsa ga hukumar ‘Yan Sanda

Wani dalibi dan 400L a jami’ar jihar Abia da ke garin Uturu, mai suna Princewill Okechukwu, yace ya shiga kungiyar asiri ne a cikin jami’a, saboda cika burinsa na zama dan siyasa bayan gama makaranta.

Kamar yadda jaridar Punch ta ruwaito, Okechukwu yana daya daga cikin wadanda ake zargi su biyar da hukumar ‘Yan Sanda ta tasa keyarsu a ofishin ma’aikatan na Umuahia, bisa ga zargin harkokin kungiyar asiri da kuma fashi da makami.

Na shiga kungiyar asiri ne don cinma burina na zama dan siyasa
Na shiga kungiyar asiri ne don cinma burina na zama dan siyasa

KU KARANTA: Obasanjo ya kalubalanci Buhari a kan rashin sanya hannu a yarjejeniyar kasuwanci na Afirka

Legit.ng ta samu labarin cewa wadanda ake zargin kwamishinan ‘Yan Sanda, Anthony Ogbizi, ne ya tasa keyar su ne a ranar Litinin, 26 ga watan Maris, a jihar.

Dalibin makarantar wanda yake aji na karshe a jami’a, mai shekara 22, wanda ke karantar nazarin kimiyyar siyasa, shine shugaban kungiyar mai suna Black Axe a jami’ar.

Wanda ake zargin yace, ya kasance a cikin kungiyar shekara daya knan, yayi nadamar cewa idan har an sakeshi bazai sake komawa harka da kungiyar asiri ba.

Wata mace da aka kama tare dasu mai suna Chika, ta nuna cewa an kamata ne bisa kuskure dan tana jiran wani ne a kusada wurin lokacin da aka kamata.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/naijcomhausa

Twitter: https://twitter.com/naijcomhausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Authors:
Aminu Ibrahim avatar

Aminu Ibrahim (Hausa HOD) Aminu Ibrahim leads the Hausa Desk at Legit.ng. He holds a Bachelor's degree in Microbiology from Ahmadu Bello University, Zaria, and pursued further with a Master's degree in Environmental Microbiology from Federal University Dutse, Jigawa. With over seven years of experience, Aminu has honed his craft in news reporting and content editing, weaving narratives that captivate and inspire audiences: aminu.ibrahim@corp.legit.ng or +2348030996164