Saurayi ya yi ma buduwarsa yankan rago bayan ta ki amincewa ta zubar da cikin da ya ɗirka mata
Wani matashi dake dalibta a kwalejin ilimin shari’a ta jihar Jigawa ya hallaka budurwarsa sakamakon kin amincewa ta zubar da cikin da take dauke shi, kamar yadda bukata, inji rahoton Daily Trust.
Majiyar Legit.ng ta ruwaito matashin mai suna Nasiru Ismail, mai shekaru 22 ya bayyana cewar shekaru takwas suka kwashe suna soyayya da Salamatu mai shekaru 22, kuma ya dauki nauyin cikin da take dauke da shi.
KU KARANTA: Rundunar Sojojin Najeriya ta sanar da shirye shiryen binne Sojoji 11 da suka mutu a Kaduna
Sai dai yace tun cikin na dna wata uku ne ya bukaci ta zubar da cikin, amma ta ki, inda bayan watanni hudu, ya kara mika mata bukatarsa na zubar da cikin, nan tace atabau, daga nan ne ya yanke shawarar kasheta tunda dai ya fahimci bata da shirin zubar da cikin.
“Na dauketa ne akan babur din wani abokina zuwa bayan gari da misalin karfe 9 na dare, inda nayi mata yankan rago, tun da dai bata amince ta zubar da cikin da nayi mata.” Inji shi.
Ku biyo mu a https://www.facebook.com/naijcomhausa
ko a http://twitter.com/naijcomhausa
KU LATSA: Hanyar sauko da sabuwar manhajar jaridar Legit.ng Hausa cikin sauki
Ga masu shawara ko korafi, a same mu a labaranhausa@corp.legit.ng
Asali: Legit.ng