Magana Ta Kare, Abba Zai Rantsar da Sabon Mataimakin Gwamnan Kano, Murtala Garo
- Gwamnan jihar Kano, Abba Kabir Yusuf zai rantsar da sabon mataimakinsa, Murtala Sule Garo a gobe Talata a gidan gwamnati
- Wannan na zuwa ne bayan Majalisar dokokin jihar ta tantance tare da amince wa da nadin Garo a matsayin mataimakin gwamna
- Gwamna Abba ya bayyana cewa nada Garo a matsayin mataimakinsa wani mataki ne na siyasa domin karfafa hadin kai a jihar
Ahmad Yusuf, kwararren edita ne a Legit Hausa da ya shafe tsawon shekaru yana kawo muku rahotannin siyasa, nishadi da al'amuran yau da kullum
Kano, Nigeria - Sabon mataimakin gwamnan jihar Kano, Mustala Sule Garo na dab da kama aiki a hukumance bayan tsallake matakan da dokar Najeriya ta gindaya.
Gwamnan Kano, Abba Kabir Yusuf, zai rantsar da Murtala Sule Garo a matsayin sabon mataimakin gwamnan jihar a ranar Talata, 5 ga watan Mayu, 2026.

Source: Facebook
Wannan na kunshe ne cikin wata sanarwa da mai ba gwamna shawara kan yada labarai, Ibrahim Adam, ya wallafa a shafin Facebook yau Litinin, 4 ga watan Mayun 2026.

Kara karanta wannan
Zambar N1.5bn: Gwamnatin Kano za ta hukunta jami'an da suka tsakure albashin ma'aikata
Gwamna Abba zai rantsar da Garo
Hadimin gwamnan ya ce za a gudanar da bikin rantsar da sabon mataimakin gwamnan da misalin karfe 11:00 na safe a dakin taro na Coronation Hall da ke gidan gwamnati a Kano.
"Mai Girma Gwamna Abba Kabir Yusuf zai rantsar da Mataimakinsa, Hon. Murtala Sule Garo a ranar Talata, 5 ga Mayu 2026 da ƙarfe 11 na safe a Coronation Hall, Gidan Gwamnati, Kano," in ji sanarwar.
Hakan na zuwa ne bayan Majalisar dokokin Kano karkashin jagorancin Rt. Hon. Jibrin Isma'ila Falgore ta tantance tare da amincewa da nadin Garo a matsayin wanda zai maye gurbin mataimakin gwamna.
Yadda Abba ya nada Murtala Sule Garo
Gwamnatin Kano ta nada Garo ne bayan murabus din tsohon mataimakin gwamna, Kwamared Aminu Abdussalam Gwarzo, wanda ya ajiye mukaminsa a ranar 27 ga Maris, 2026.
Rahotanni sun nuna cewa rikici tsakaninsa da Gwamna Abba Gida-Gida musamman kan kin sauya sheka daga NNPP zuwa APC, ne ya jawo murabus din.

Kara karanta wannan
Ganduje, manyan APC sun saya wa Abba fam, an tara N50bn don takarar Tinubu a 2027
An kuma ambaci zarge-zargen cin hanci da kuma shirin tsige shi daga majalisar dokokin jihar ta fara yi a matsayin wasu daga cikin dalilai, duk da cewa ya ce murabus dinsa ba yana nufin ya amince yana da laifi ba ne.
Takaitaccen bayani kan Murtala Garo
Murtala Sule Garo ya taba rike mukamin kwamishinan kananan hukumomi da harkokin masarautuna jihar Kano a lokacin gwamnatin tsohon gwamna, Drm Abdullahi Umar Ganduje.
Haka kuma shi ne dan takarar mataimakin gwamna na jam’iyyar APC a zaben 2023, wanda suka sha kaye a hannun Gwamna Abba Kabir Yusuf.

Source: Facebook
Majalisar dokokin jihar Kano ta tabbatar da nadinsa a makon da ya gabata bayan tantance dhi kamar yadda kundin tsarin mulkin Najeriya ya tanada.
Gwamna Abba ya bayyana cewa zaben Garo a matsayin mataimakinsa wani mataki ne na siyasa domin karfafa hadin kai da kuma fadada goyon baya a fadin jihar.
An saya wa Gwamna Abba fam din APC
A wani labarin, kun ji cewa jiga-jigan jam'iyyar APC a Kano sun saya wa Gwamna Abba Kabir Yusuf fam domin ya nemi takara karo na biyu gabanin zaben 2027.
An sanar da haka ne a wani taro da aka gudanar a Kano, inda shugabannin jam’iyyar APC suka tabbatar da cikakken amincewarsu da jagoranci da ayyukan Gwamna Abba.
A nasa bangaren, gwamna Abba Kabir Yusuf ya gode da wannan karamci, inda ya sake jaddada kudirinsa na tafiyar da mulki mai hada kowa da kowa.
Asali: Legit.ng