'Yan Bindiga Sun Kai Harin Ramuwar Gayya a Katsina, an Kashe Bayin Allah

'Yan Bindiga Sun Kai Harin Ramuwar Gayya a Katsina, an Kashe Bayin Allah

  • Jami'an tsaro sun ragargaji 'yan bindiga bayan sun samu bayanan sirri kan ayyukansu a jihar Katsina da ke yankin Arewa maso Yamma
  • Jami'an tsaro sun yi nasarar kashe wasu daga cikin 'yan bindigan tare da kwato kayayyaki masu muhimmanci a hannunsu
  • Sai dai, daga baya 'yan bindigan sun kai harin ramuwar gayya inda suka hallaka mutanen da ba su san hawa ba, ba su san sauka ba

​​​​​​​​Editan Legit Hausa Sharif Lawal yana da kwarewar shekaru wajen kawo rahotannin siyasa, al'amuran yau da kullum, tsegumi da nishadi

Jihar Katsina - 'Yan bindiga sun kashe mutane 11 a ƙauyen Gwalgoro da ke karamar hukumar Kankia a jihar Katsina.

An kashe mutanen ne biyo bayan wani harin ɗaukar fansa da ake zargin ’yan bindiga suka kai, sa’o’i kaɗan bayan jami’an tsaro sun yi nasarar dakile wani hari tare da kashe mambobinsu da dama.

'Yan bindiga sun kai harin ramuwar gayya a Katsina
Gwamnan jihar Katsina, Dikko Umaru Radda Hoto: Ibrahima Kaulaha Mohammed
Source: Facebook

Jaridar Daily Trust ta kawo rahoton cewa kwamishinan tsaron cikin gida da harkokin cikin gida, Nasiru Mu’azu, ya tabbatar da hakan cikin wata sanarwa a ranar Lahadi, 3 ga watan Mayun 2026.

Kara karanta wannan

'Yan bindiga sun farmaki 'yan sanda a Kwara, an samu asarar rayuka

An samu nasara kan 'yan bindiga

Kwamishinan ya miƙa ta’aziyya ga iyalai da dangin waɗanda abin ya shafa tare da yin tir da harin.

A cewar sanarwar, tashin hankalin ya fara ne a ranar Asabar, 2 ga watan Mayu, 2026, lokacin da rahotannin sirri suka bayyana cewa wani sanannen jagoran ’yan bindiga, Mohammadu Fulani, ya jagoranci tawaga zuwa wasu muhimman gadoji a ƙaramar hukumar Kankia da nufin aikata laifi.

Bayan samun wannan bayani, mambobin al’ummar yankin sun sanar da hukumomin tsaro. Daga nan DPO na Kankia ya tura jami’ai tare da jagorantar rundunar haɗin gwiwa ta jami’an tsaro domin tunkarar maharan.

Jami’an tsaron sun yi artabu da ’yan bindigan, inda suka kashe da dama daga cikinsu tare da ƙwato babura takwas da kuma shanu da aka sato.

Sanarwar ta bayyana cewa kayayyakin da aka ƙwato suna hannun ƴan sanda a halin yanzu, tashar Channels tv ta kawo rahoton.

'Yan bindiga sun kai harin ramuwar gayya

Kara karanta wannan

Sojoji sun kashe kwamandojin 'yan ta'adda a Katsina, an kwato makamai da kudade

A cewar kwamishinan, ’yan bindigan sun sake haɗuwa daga baya, kuma a matsayin martani ga asarar da suka yi, sun ƙaddamar da wani sabon hari a ƙauyen Gwalgoro da ke gundumar Gyaza/Kunduru da tsakar rana.

Yayin harin, an kashe mazauna ƙauyen guda 11 a cikin abin da gwamnati ta siffanta da “harin matsorata kan fararen hula marasa laifi.”

Gwamnati ta yi Allah wadai da harin

Gwamnatin jihar ta yi Allah-wadai da kisan, inda ta bayyana karkata akalar hare-hare zuwa kan fararen hula a matsayin abin da ba za a amince da shi ba kuma aikin ta’addanci ne.

'Yan bindiga sun kashe mutane a Katsina
Taswirar jihar Katsina, tarayyar Najeriya Hoto: Legit.ng
Source: Original

Ta yaba wa jami’an tsaro saboda yadda suka mayar da martani cikin gaggawa wajen dakile harin farko, sannan ta buƙaci mazauna yankin da su ci gaba da kasancewa cikin shiri da kuma ba wa jami’an tsaro bayanai akan lokaci.

Kwamishinan ya kuma jaddada ƙudurin gwamnati na yaƙar rashin tsaro da kuma kare rayuka da dukiyoyi a faɗin jihar.

Batun tattaunawa da 'yan bindiga a Arewa

A wani labarin kuma, kun ji cewa gwamnan jihar Sokoto, Ahmad Aliyu, ya bayyana matsayar gwamnonin jihohin Arewa maso Yamma, kan tattaunawa da 'yan bindiga.

Kara karanta wannan

Dakarun sojoji sun ritsa 'yan ta'adda a Borno, an kashe tsageru

Gwamna Ahmad Aliyu ya bayyana cewa gwamnonin sun cimma matsayar cewa ba za su tattauna da 'yan bindiga ba.

Sai dai, ya jaddada cewa abu daya kawai da za su yarda da shi daga wajen 'yan bindiga shi ne su ajiye makamansu ba tare da wani sharadi ba.

Asali: Legit.ng

Authors:
Sharif Lawal avatar

Sharif Lawal (Hausa Editor) Sharif Lawal ma'aikacin jarida ne wanda ya samu gogewa a harkar aikin jarida. Ya yi digirinsa na farko a jami'ar Ahmadu Bello (ABU) da ke Zaria. Ya samu horo daga Reuters kan aikin jarida da tantance labarai. Za a iya tuntubarsa ta Sharif.lawal@corp.legit.ng