Atiku da Shugabannin ADC Sun Fara Shirin Bin Kwankwaso zuwa NDC? Gaskiya Ta Fito
- Tsohon mataimakin shugaban kasa, Atiku Abubakar da shugahannin ADC sun musanta zargincewa suna shirin komawa jam'iyyar NDC
- Mai magana da yawun Atiku, Paul Ibe ya ce jita-jitar da ake yadawa ba gaskiya ba ne, babu wani shiri na sauya jam'iyya a halin yanzu
- Wannan dai na zuwa ne bayan Sanata Kwankwaso da Peter Obi sun koma NDC, saboda rikicin da ya dabaibaiye jam'iyyar ADC
Ahmad Yusuf, kwararren edita ne a Legit Hausa da ya shafe tsawon shekaru yana kawo muku rahotannin siyasa, nishadi da al'amuran yau da kullum
Abuja, Nigeria– Jam’iyyar ADC tare da magoya bayan tsohon mataimakin shugaban kasa, Atiku Abubakar, sun musanta rahotannin da ke cewa suna tattaunawar sauya sheka zuwa jam’iyyar NDC.
Bayan sauya shekar tsofaffin yan takarar shugaban kasa, Sanata Rabiu Kwankwaso da Peter Obi, an fara rade-radin cewa ADC da Atiku na duba yiwuwar bin sahunsu zuwa NDC.

Source: Facebook
Amma rahoton da jaridar Vanguard ta wallafa yau Litinin, ya nuna cewa wannan jita-jita ba gaskiya ba ce, ADC da Alhaji Atiku ba su da wani shiri da kulla sabuwar hadaka.
Wannan martani na zuwa ne yayin da jam’iyyar ADC ke fuskantar kalubale na cikin gida kan shugabanci da kuma yadda za ta hada kan jam’iyyun adawa gabanin zaben gaba.
Da gaske Atiku na shirin shiga NDC?
Mai ba Atiku shawara kan harkokin yada labarai, Paul Ibe, ya shaida cewa babu irin wannan tattaunawa da ta shafi tsohon mataimakin shugaban kasa ko tsohon gwamnan jihar Osun, Rauf Aregbesola.
“Idan har akwai irin wannan magana ta shirin komawa NDC, ni ne zan fara sani. Ban yarda cewa akwai hakan ba," in ji shi.
ADC ta yi watsi da jita-jitar
Wasu daga cikin shugabannin jam’iyyar ADC sun fito sun yi watsi da rahotannin, suna mai cewa babu wata tattaunawar yiwuwar hada kai tsakanin manyan jiga-jigan ADC da NDC.

Kara karanta wannan
An gudu ba a tsira ba: Guguwa ta tunkaro NDC awanni da sauya sheƙar Kwankwaso da Obi
A rahoton jaridar Punch, sakataren yada labarai na jam’iyyar ADC na kasa, Bolaji Abdullahi, ya bayyana rahotannin a matsayin “karya tsagwaronta.”
Duk da haka, rahotanni sun nuna cewa ana zargin akwai tattaunawa tsakanin wasu manyan ’yan siyasa a ADC da shugabannin NDC, tare da hasashen cewa za a iya sanar da wani matsaya nan da tsakiyar mako.

Source: Twitter
Ana zargin ADC za ta hada kai da NDC
Bayan rahoton sauya shekar Peter Obi da Rabiu Musa Kwankwaso zuwa NDC, ana ganin jam’iyyar a matsayin wata sabuwar mafaka ga ’yan adawa da ke neman sabon hadin kai.
Wasu majiyoyi sun ce duk wata tattaunawa da ake yi ba lallai ta zama ta sauya jam’iyya kai tsaye ba, sai dai wani yunkuri na kafa hadakar ’yan adawa gabanin zaben 2027.
ADC ta shirya zaben fitar da 'dan takara
A wani rahoton, kun ji cewa jam'iyyar ADC mai adawa a Najeriya ta shirya gudanar da zaben fitar da gwani domin tunkarar zaben shekarar 2027.
Jam'iyyar ADC ta sanya ranar 25 ga Mayu, 2026, don zaɓen fidda gwani na ɗan takarar shugaban ƙasa, sannan ta sanya farashin fom ɗin tsayawa takara a kan Naira miliyan 100.
ADC ta ce jadawalin ya tsara ƙa’idoji da buƙatun tsayar da ’yan takara gabanin babban zaɓen 2027, inda ta jaddada ƙudurinta na bin tsarin dimokuradiyya.
Asali: Legit.ng
