Yadda yan Boko Haram suka saci wata mace mai ciki har ta haihu a hannunsu, suka rada ma yaron suna

Yadda yan Boko Haram suka saci wata mace mai ciki har ta haihu a hannunsu, suka rada ma yaron suna

Wani matashi mai suna Isah Danladi Gulaj dan asalin karamar Dikwa na jihar Borno ya bayyana irin tashin hankalin da ya gamu da shi sakamakon wani hari da mayakan Boko Haram suka kai ma iyalinsa.

Isah yace wannan lamari ya faru ne a lokacin da yan Boko Haram suke rikeda garin Bama, inda a lokacin maza ke shawara da iyalansu akan zasu tafi cikin Maiduguri, idan sun isa lafiya, sai su gayyaci matan su biyo sawunsu, don gudun kada Boko Haram su tare su.

KU KARANTA: Ba zan je Kotu ba saboda ana gwamnan jiharmu ya shirya kashe ni – Inji wani Sanata

Isah ya bayyana haka ne cikin wata hira da yayi da Nasiru Adamu El-Hikaya, inda yace bayan maza basa tafiya da mata ne saboda idan Boko Haram sun nemi tare su, zasu iya tserewa amma, mata ba zasu iya ba.

Don haka yace bayan ya isa Maiduguri, tafiyan kwanaki uku, sai ya aika ma matarsa toh ya isa lafiya, don haka zata iya tahowa, fitarta ke da wuya tare da sauran mata, sai yan ta’addan suka tare ta, inda suka tambaye ta inda zata, bayan ta fada musu, sai suka ce ai Maiduguri garin arna ne, don haka sun kamata ganima.

Isah ya bayyana ma majiyar Legit.ng cewa ya bar matarsa da ciki, don kwatakwata watanni shidda kenan da aurensu, amma yace daga bisani ya samu labarin ta haihu a hannu yan Boko Haram, inda suka rada ma yaron nasa suna Muhammad.

Daga karshe yace wannan ne daliln da yasa ya tattara inasa inasa ya koma zama a babban birnin tarayya Abuja, inda a yanzu sama da shekara daya da rabi kenan bai sake jin labarin matarsa da dansa ba.

Ku biyo mu a https://www.facebook.com/naijcomhausa

ko a http://twitter.com/naijcomhausa

KU LATSA: Hanyar sauko da sabuwar manhajar jaridar Legit.ng Hausa cikin sauki

Ga masu shawara ko korafi, a same mu a labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Authors:
Mudathir Ishaq avatar

Mudathir Ishaq Mudathir Ishaq is the head of the Hausa desk at Legit.ng. He studied Industrial Chemistry as first degree at the University of Abuja, Journalism (CSR Specialization) with the Michigan State University and runs MSc Industrial Chemistry from the Nasarawa State University, Keffi. With more than a decade experience in news reporting and content editing, he has interviewed influential personalities. He can be reached on: mudathir.ishaq@corp.legit.ng

Tags: