Ganduje na daf da kammala titin kasan da ake yi a Kofar Ruwa
- Gwamnatin Ganduje za ta karasa wani aiki da Kwankwaso ya fara a baya
- Ana sa rai kwanan nan a kammala aikin titin kasa da ake yi a Kofar ruwa
- Bayan nan kuma akwai wasu ayyuka da dama da Ganduje yake yi a Kano
Mun samu labari daga Jaridar Daily Trust cewa Gwamnatin Jihar Kano tayi nisa kwarai da gaske a wani aiki da ake ta faman yi na titin kasa a Unguwar Kofar Ruwa a cikin karamar Hukumar Dala Garin Kano.
A farkon makon nan ne Shugaban Kwamitin ayyuka a Majalisar dokokin Jihar Kano Ibrahim Gana da ke wakiltar mazabar Nasarawa ya bayyana cewa an ci sama da kashi 80% na titin kasan da ake ginawa a Kofar Ruwa.
KU KARANTA: Ana neman Shehu Sani ya sauya sheka zuwa PDP
'Dan Majalisar ya bayyana wannan ne lokacin da yake duba wasu ayyuka na Gwamnan Jihar Kano Dr. Abdullahi Umar Ganduje a cikin Nasarawa da kuma Kumbotso. Ana sa rai za a gama aikin ne nan da 'Yan watanni kadan.
An dai biya 'Dan kwangilar da ke aikin titin kasar kashi 70% na kudin sa kuma za a cika masa kason sa da zarar an gama aiki. 'Yan Majalisar sun kuma duba wata hanyar kasar sa ake yi ta Madobi zuwa Pan-shekara a Garin Kumbotso.
Idan ka na da wata shawara ko bukatar ba mu labari, a tuntube mu a labaranhausa@corp.legit.ng
Ku same mu a https://www.facebook.com/naijcomhausa Ko a http://twitter.com/naijcomhausa
Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en
Asali: Legit.ng