Yan bindiga sanye da Hijabai sun yi garkuwa da wasu manyan Mata guda 2 a Katsina

Yan bindiga sanye da Hijabai sun yi garkuwa da wasu manyan Mata guda 2 a Katsina

Wata sabuwa inji yan caca, wasu miyagu masu garkuwa da mutane dauke da muggan makamai sun yi shigar burtu, inda suka sanya kayan mata, suka afka cikin wani gida, suka yi awon gaba da wasu iyaye mata guda biyu a jihar Katsina.

Daily Trust ta ruwaito wannan lamari ya faru ne a garin Malumfashi na jihar, inda yan bindigan suka afka gidan Ahmed Mahuta sanye da hijabai da misalin karfe 10 na dare, suka saci manyan mata guda biyu, Hajiya Duduwa da Hajiya Aisha.

KU KARANTA: Sanata Dino Melaye ya dawo Najeriya, ya halarci zaman majalisar dattawa

Majiyar Legit.ng ta ruwaito daga bisani yan bindigan sun sako Hajiya Aisha, sakamakon tabarbrewar lafiyarta, amma sun yi awon gaba da diyarta Hajiya Duduwa.

Rahotanni sun tabbatar da cewar Hajiya Aisha mahaifiyace ga tsohon babban jami’I a hukumar zabe mai zaman kanta, INEC, Hussaini Mahuta, da kuma darakta a hukumar NIMASA, Gambo Mahuta.

Sai dai tuni masu garkuwan sun nemi iyalan Duduwa da su biya kudin fansa na naira miliyan 300, idan har suna kaunar su sake ganinta. Majiyarmu tayi iya bakin kokarin jin ta bakin rundunar Yansandan jihar Katsina game da batun, amma Kaakakinsu DSP Gambo Isah bai ce uffan ba.

Ku biyo mu a https://www.facebook.com/naijcomhausa

ko a http://twitter.com/naijcomhausa

Ga masu shawara ko korafi, a same mu a labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Authors:
Mudathir Ishaq avatar

Mudathir Ishaq Mudathir Ishaq is the head of the Hausa desk at Legit.ng. He studied Industrial Chemistry as first degree at the University of Abuja, Journalism (CSR Specialization) with the Michigan State University and runs MSc Industrial Chemistry from the Nasarawa State University, Keffi. With more than a decade experience in news reporting and content editing, he has interviewed influential personalities. He can be reached on: mudathir.ishaq@corp.legit.ng