An Gabatar da Bidiyo a Kotu, Mutum 2 Suna da Masaniyar Shirin Yi wa Tinubu Juyin Mulki
- An gabatar da bidiyon tambayoyin da jami'an tsaro suka yi wa wadanda ake tuhuma da hannu a kitsa juyin mulki, a zaman kotu na yau Litinin
- Mutum biyu daga wadanda ake zargi sun tabbatar da cewa sun samu labarin shirin kifar da gwamnatin Tinubu amma ba su ba da goyon baya ba
- Lauyoyin wadanda ake tuhuma sun kalubalanci bidiyon da bangaren gwamnati suka gabatar, inda suka ce da yiwuwar ba da som rai suka amsa ba
Ahmad Yusuf, kwararren edita ne a Legit Hausa da ya shafe tsawon shekaru yana kawo muku rahotannin siyasa, nishadi da al'amuran yau da kullum
Abuja – Babbar kotun tarayya da ke Abuja ta kalli bidiyon tambayoyin bincike da aka yi wa uku daga cikin mutane shida da ake tuhuma da yunkurin kifar da gwamnatin Shugaba Bola Ahmed Tinubu.
A cikin bidiyon da aka nuna a zaman kotu, biyu daga cikin wadanda ake tuhuma sun tabbatar wa jami'an tsaro cewa suna da masaniyar shirin yi wa Bola Tinubu juyun mulki.

Source: Twitter
Mutum 2 sun san da shirin juyin mulki
The Nation ta ce wadanda suka amsa sune tsohon kyaftin na rundunar sojin ruwa, Erasmus Ochegobia Victor da sufeton ‘yan sanda, Ahmed Ibrahim yayin da tsohon Manjo Janar Mohammed Ibrahim Gana ya ce bai san komai ba.
An gabatar da bidiyon ne a cikin wani faifan ajiya da bangaren gwamnati suka gabatar, amma lauyoyin wadanda ake tuhuma sun kalubalanci karbarsa a matsayin shaida.
Sun kuma yi adawa da nuna bidiyon tun farko, amma Mai shari’a Joyce Abdulmalik ta yi watsi da korafinsu tare da umartar a nuna shi, tana mai cewa wannan al’ada ce a irin wadannan shari’o’i.
Ta kara da cewa za a gudanar da wata karamar shari’a a cikin shari’ar domin tantance ko wadanda ake tuhuma sun yi furucin da son ransu ko tursasa masu aka yi.
Abin da wadanda ake zargin suka fada
A cikin bidiyon, Gana ya ce ya yi ritaya daga rundunar sojin Najeriya a shekarar 2010 kuma yana rayuwa cikin nutsuwa tun daga lokacin.

Kara karanta wannan
'Yan Najeriya sun rikita Amurka da damfara, sun wawure miliyoyin daloli a jihohi 47
Ya amince cewa ya san wanda ake zargi da jagorantar shirin, Kanal M. A. Ma’aji, amma ya ce sam bai san yana shirin juyin mulki ba.
Ya kuma bayyana cewa an danganta sunansa da wasu kudade da aka tura Naira miliyan biyu, da kuma yada wani jawabin juyin mulki ta WhatsApp, amma ya ce kawai ya tura abin da ya samu ne ba tare da gyara ko kirkira ba.
Gana ya musanta zargin cewa ya yi leken asiri a fadar shugaban kasa ko kuma ya taimaka wajen tara kudade domin yin juyin mulki, cewar rahoton Premium Times.

Source: Getty Images
Shi kuwa Victor ya amince cewa ya san Ma’aji kuma ya san da shirin kifar da gwamnati, amma bai kai rahoto ga hukumomi ba saboda dangantakar da ke tsakaninsu.
Ya ce Ma’aji ya taba bayyana masa cewa yana son kifar da gwamnati saboda rashin samun karin girma, amma dai ya shawarce shi da ya yi ritaya maimakon shiga irin wannan aiki.
Ya kuma amince cewa an nemi ya bayar da gudummawar kudi ko taimakawa wajen tara kudade, amma ya ki shiga cikin shirin.

Kara karanta wannan
Kotu ta amince da bukatar gwamnatin Tinubu a shari'ar mutane 6 da ake zargi da shirin juyin mulki
Kotu ta dage zaman shari'a
Masu bincike sun bayyana cewa an dauki bidiyon ne domin tabbatar da cewa an yi furucin ba tare da tilas ba.
An kuma sanar da wadanda ake tuhuma cewa suna da ‘yancin yin shiru idan suka ga dama, daga nan kotu ta dage ci gaba da sauraron shari’ar zuwa gobe Talata da karfe 11:00 na safe.
Kotu ta amince a boye bayanan shaida
A wani labarin, kun ji cewa kotun ta amince da bukatar gwamnatin tarayya na boye suna da asalin wata shaida daga rundunar sojoji a shari'ar wadanda ake zargi da kitsa juyin mulki.
Mai shari’a Joyce Abdulmalik ce ta yanke wannan hukunci bayan sauraron hujjojin lauyan gwamnati, Rotimi Oyedepo (SAN), da kuma lauyoyin masu kare wadanda ake tuhuma.
Wasu mutane uku daga Jaiz Bank, SunTrust Bank da Providus Bank sun gabatar da bayanansu, kuma kotu ta karbe su a matsayin shaidu.
Asali: Legit.ng
