Buhari mutumin kirki ne, kada kuyi watsi da shi – Dan uwan Martin Luther King Jr ya gargadi yan Najeriya

Buhari mutumin kirki ne, kada kuyi watsi da shi – Dan uwan Martin Luther King Jr ya gargadi yan Najeriya

Dan uwan marigayi Martin Luther King Jr, Isaac newton-Farris Jnr, ya yi kira gay an Najeriya da su bada hadin kai da shugaba Muhammadu Buhari wajen karashe ayyukan da ya fara domin gina Najeriya.

Farris ya bayyana hakan ne a wani hira da manema labarai a Abuja bayan ganawarsa da shugaba Buhari a wani liyafa da aka shirya musu a fadar shugaban kasa.

Yace: “Shawarana ga yan Najeriya shine, na san yadda yan Najeriya ke ji, ba su dadin shugaba Buhari yadda yake gudanar da abubuwa cikin sanyi.

“Ina baiwa yan Najeriya shawara su baiwa wannan bawan Allah lokaci domin yin aikin da yake yi. Shine shugaba mafi ingancin da wannan nahiya ta taba samarwa.

Buhari mutumin kirki ne, kada kuyi watsi da shi – Dan uwan Martin Luther King Jr ya gargadi yan Najeriya
Buhari mutumin kirki ne, kada kuyi watsi da shi – Dan uwan Martin Luther King Jr ya gargadi yan Najeriya

“Ina baku tabbacin cewa idan kuka rike shi, zai mayar da Najeriya wuri alfahari.”

“Kun san mutumin kirki ne amma idan kukayi tunanin zai dinga amfani da karfinsa wajen ladabta masu rashawa ba tare da bin doka ba, mai zai faru idan wani mara mutunci ya zama shugaba gobe?”

KU KARANTA: Yan bindigan da ke yiwa Dino Melaye aiki sun arce daga kurkukun yan sanda

Yan uwan marigayi Martin Luther King din sun baiwa shugaba Buhari lambar yabo kan ingantaccen shugabanci.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/naijcomhausa Twitter: https://twitter.com/naijcomhausa

Asali: Legit.ng

Authors:
Mudathir Ishaq avatar

Mudathir Ishaq Mudathir Ishaq is the head of the Hausa desk at Legit.ng. He studied Industrial Chemistry as first degree at the University of Abuja, Journalism (CSR Specialization) with the Michigan State University and runs MSc Industrial Chemistry from the Nasarawa State University, Keffi. With more than a decade experience in news reporting and content editing, he has interviewed influential personalities. He can be reached on: mudathir.ishaq@corp.legit.ng