Bayan Hukuncin Kotun Koli, Majalisar BoT Ta Nada Sabon Shugaban Jam'iyyar PDP na Kasa
- Majalisar amintattu ta PDP (BoT) ta nada kwamitin rikon kwarya karkashin jagorancin tsohon ministan ayyuka na musamman, Tanimu Turaki
- Ta dauki wannan mataki ne a taron Majalisar Zartarwa (NEC) da tsagin Turaki suka gudanar a Abuja bayan hukuncin kotun koli
- Shugaban BoT, Sanata Adolphus Wabara ya ce kwamitin rikon kwarya zai karbi ragamar tafiyar da harkokin jam'iyyar kafin a shirya zabe
Ahmad Yusuf, kwararren edita ne a Legit Hausa da ya shafe tsawon shekaru yana kawo muku rahotannin siyasa, nishadi da al'amuran yau da kullum
Abuja – Majalisar amintattu ta jam’iyyar PDP (BoT) karkashin jagorancin Sanata Adolphus Wabara ta fara kokarin daukar rmatakan da suka dace bayan hukuncin Kotun Koli.
Majalisar BoT ta sanar da nada kwamitin gudanarwa (NWC) na rikon kwarya mai mambobi 13 domin tafiyar da harkokin jam’iyyar adawa ta PDP.

Source: Twitter
Turaki ya zama shugaban PDP na riko
A rahoton Channesl tv, Wabara ya ce an dauki wannan mataki ne bisa tanadin kundin tsarin mulkin PDP, yana mai cewa hukuncin kotun koli da ya tabbatar da soke taron Ibadan ya haifar da gibi a shugabancin jam’iyyar.

Kara karanta wannan
An gudu ba a tsira ba: Guguwa ta tunkaro NDC awanni da sauya sheƙar Kwankwaso da Obi
An nada tsohon minista kuma tsohon shugaban jam’iyyar, Tanimu Turaki, a matsayin mukaddashin shugaban PDP na kasa, watau shugaban kwamitin rikok iwarya.
PDP ta gudanar da taron NEC a Abuja
An cimma wannan matsaya ne a wani taron kwamitin zartarwa na kasa (NEC) da bangaren Tanimu Turaki na jam’iyyar PDP ya gudanar a cibiyar Yar’Adua da ke Abuja.
Manyan jiga-jigan jam’iyyar da suka halarci taron sun hada da gwamnan jihar Oyo, Seyi Makinde; tsohon ministan ayyuka na musamman, Tanimu Turaki; da tsohon gwamnan jihar Neja, Babangida Muazu.
Sauran sun hada da tsohon ministan yada labarai, Farfesa Jerry Gana; Sanata Adolphus Wabara; da tsohuwar ministar harkokin mata, Zainab Maina da sauransu.
An sake soke shugabancin tsagin Wike
Bangaren ya kuma jaddada cewa taron jam’iyyar PDP da aka gudanar a Abuja wanda ya samar da kwamitin gudanarwa karkashin Abdulrahman Mohammed ba shi da inganci, cewar rahoton The Cable.
Sun bayyana cewa bisa tsarin mulkin PDP, dole ne a kafa kwamitin rikon kwarya idan aka samu gibi a shugabanci, wanda ya sa suka bukaci kwamitin amintattu ya dauki wannan mataki.

Source: Twitter
A ranar Alhamis, Kotun Loli ta rushe babban taron da PDP ta gudanar a Ibadan, babban birnin jihar Ibadan, wanda aka zabi Tanumu Turaki a matsayin shugaban jam'iyya.
Hakan da ya sa majalisar BoT ta iria zaman gaggawa domin nazari da daukar mataki kan gibin shugabanci a PDP, inda ta nada kwamitin rikon kwarya a taron NEC yau Litinin.
Gwamnan Bauchi ya fice daga PDP
An ji cewa gwamnan Bauchi, Bala Mohammed, ya sanar da ficewarsa daga jam'iyyar PDP mai adawa a Najeriya bayan hukuncin Kotun Koli.
Majiyoyi suka ce gwamnan ya fice ne tare da magoya bayansa masu biyayya ga bangaren Tanimu Turaki kwanaki biyu bayan hukuncin Kotun Koli kan rikicin shugabanci.
Sanata Bala Mohammed ya bayyana cewa ba zai yi takarar shugaban kasa ba a 2027, domin a PDP ma sun mayar da batun tsayawa takara zuwa Kudu.
Asali: Legit.ng
