Sakon Kwankwaso ga 'Yan Najeriya bayan Sauya Sheka zuwa Jam'iyyar NDC daga ADC
- Jagoran Kwankwasiyya, Sanata Rabiu Musa Kwankwaso, ya sauya sheka zuwa jam'iyyar NDC a hukumance
- Sanata Kwankwaso ya yi nuni da cewa ya sauya zuwa jam'iyyar bayan ya lura suna da manufofi iri daya da na shi
- Tsohon dan takarar shugaban kasar a zaben 2023 ya kuma yi kira ga magoya bayansa da su yi rajista da sabuwar jam'iyyar
CHECK OUT: How to Start Earning with Copywriting in Just 7 Days – Even if You’re a Complete Beginner
Editan Legit Hausa Sharif Lawal yana da kwarewar shekaru wajen kawo rahotannin siyasa, al'amuran yau da kullum, tsegumi da nishadi
FCT, Abuja - Tsohon dan takarar shugaban kasa a zaben 2027, Rabiu Musa Kwankwaso, ya aika da sako ga magoya bayansa bayan shiga jam'iyyar NDC.
Sanata Rabiu Musa Kwankwaso ya buƙaci magoya bayansa da su yi rajista da jam’iyyar NDC wadda ya sauya sheka zuwa cikinta.

Source: Facebook
Rabiu Kwankwaso ya bayyana hakan ne a wani rubutu da ya yi a shafinsa na X a ranar Litinin, 4 ga watan Mayun 2026.
Kwankwaso da Obi sun bar ADC
Kwankwaso da Peter Obi, sun shiga jam’iyyar NDC ne a ranar Lahadi, 3 ga watan Mayun 2026 bayan sun fice daga jam’iyyar ADC.
Sun ce sun fice daga ADC ne sakamakon rashin tabbas game da makomar jam’iyyar biyo bayan hukuncin Kotun Koli na ranar 30 ga watan Afrilun 2026.
Jaridar TheCable ta ce Cleopas Moses Zuwoghe, shugaban jam’iyyar NDC na ƙasa, shi ne ya miƙa wa Obi da Kwankwaso katin zama mambobin jam’iyyar.
Meyasa Kwankwaso da Obi suka koma NDC?
Da yake jawabi bayan taron, Kwankwaso ya ce shi da Peter Obi sun je wurin ne domin tattauna batun jam’iyyar da kuma akidunta tare da masu ruwa da tsaki na NDC.
Tsohon ministan ya bayyana cewa sun fahimci cewa akidojinsu iri ɗaya ne, sannan ya buƙaci ’yan Najeriya da su yi rajista da NDC kafin cikar wa’adin rajistar mambobin jam’iyyar.
Me Kwankwaso ya ce bayan shiga NDC?

Kara karanta wannan
An gudu ba a tsira ba: Guguwa ta tunkaro NDC awanni da sauya sheƙar Kwankwaso da Obi
A saƙon da ya wallafa a ranar Litinin, Kwankwaso ya ce jam’iyyar za ta iya ceto ’yan Najeriya.
“Jiya, mun ɗauki gagarumin mataki na haƙiƙa ta hanyar shiga jam’iyyar NDC a hukumance."
“A gidan Sanata Seriake Dickson da ke Abuja, na sanar da cewa shawararmu ta samo asali ne daga tsantsar sadaukarwa ga dabi’un dimokuradiyya."
“Mun ƙuduri aniyar samar wa mutanenmu sahihin dandamali inda za su iya bunkasa tare da cimma burinsu gaba ɗaya."
“Sakamakon haka, ina kira ga dukkan magoya bayanmu masu kishin ƙasa da kuma ’yan Najeriya nagari da su shiga NDC su tsaya tare da mu a cikin wannan sabon yaƙi na samar da shugabanci nagari da ingantacciyar dimokuradiyya.”
- Rabiu Musa Kwankwaso

Source: Twitter
Kwankwaso ya shiga ADC ne a ranar 30 ga watan Maris bayan ya yi murabus daga jam’iyyar NNPP, wadda ya yi amfani da ita wajen takarar shugaban ƙasa a zaɓen 2023.
Peter Obi ya fice daga jam'iyyar ADC
A wani labarin kuma, kun ji cewa tsohon dan takarar shugaban kasa a zaben 2023, Peter Obi, ya sake sauya sheka daga jam'iyyar da yake ciki.
Peter Obi, wanda ya kasance tsohon gwamnan jihar Anambra ne, ya bayyana cewa ya yanke shawarar barin jam'iyyar ADC.
Tsohon jigon na ADC ya bayyana cewa daukar wannan mataki ya zama dole duk da cikas da matsin lamba da yake fuskanta.
Asali: Legit.ng

