Manyan ‘Yan siyasan da Atiku zai iya tsaidawa a kujerar Mataimakin Shugaban kasa

Manyan ‘Yan siyasan da Atiku zai iya tsaidawa a kujerar Mataimakin Shugaban kasa

Bisa dukkan alamu Atiku Abubakar zai jarraba sa’ar sa a PDP a zaben 2019. Kafin nan Atiku ya fito takara a 1992, 2007, 2011 da kuma 2015. Yanzu dai an fara harsashen yadda zaben zai kasance.

Mun kawo maku jerin wasu ‘Yan siyasar kasar nan da mu ke tunanin Wazirin Adamawa Atiku zai iya zaba a domin su yi takarar Mataimakin Shugaban kasa a zabe mai zuwa na 2019 karkashin Jam’iyyar PDP.

Manyan ‘Yan siyasan da Atiku zai iya tsaidawa a kujerar Mataimakin Shugaban kasa
Tsohon Mataimakin Shugaban kasa Atiku zai sake takara

1. Ayo Fayose

Gwamnan Ekiti Ayo Fayose na neman takarar Shugaban kasa sai dai hakan zai yi masa wahala ganin bai fito daga Yankin Arewa ba. A lokacin Fayose ya bar ofis kuma zai iya fitowa a matsayin Mataimakin Atiku Abubakar.

Manyan ‘Yan siyasan da Atiku zai iya tsaidawa a kujerar Mataimakin Shugaban kasa
Gwamna Ayo Fayose yana neman takarar Shugaban kasa

2. Ike Ekweremadu

Shi kuma Ekweremadu ya fito ne daga Yankin Inyamurai wanda Atiku yake ta kokarin jawo hankalin su da kiran yi wa Najeriya garambuwal. Mataimakin Shugaban Majalisar Dattawan ba zai ki wannan tayi idan ta kama ba.

KU KARANTA: Atiku ya kaddamar da shirin takarar Shugaban kasa

3. Godswill Akpabio

Tsohon Gwamnan na Akwa Ibom shi ne shugaban marasa rinjaye a Majalisar Dattawa. Sanatan yana da karfi a PDP musamman a Kudancin kasar nan don haka ba mamaki idan Wazirin na Adamawa ya tsaida shi Mataimaki.

Manyan ‘Yan siyasan da Atiku zai iya tsaidawa a kujerar Mataimakin Shugaban kasa
Atiku Abubakar zai iya tsaida Agbaje Mataimakin sa

4. Jimi Agbaje

Shi kuam Agbaje ya fito ne daga kasar Yarbawa kamar Ayo Fayose. Tsohon ‘Dan takarar Gwamnan na Legas yana da nagarta da kuma kima don haka ba mamaki Atiku yayi amfani da shi idan ya tsaya takara a zaben 2019.

5. Nyesom Wike

Gwamnan na Jihar Ribas yana cikin wanda su ka fi kowa karfi yanzu a Jam’iyyar adawar ta PDP. Ba abin mamaki bane idan Atiku Abubakar ya nemi ya fito takara da Gwamnan na Kasar Neja-Delta mai arzikin man fetur.

Idan ka na da wata shawara ko bukatar ba mu labari, a tuntube mu a labaranhausa@corp.legit.ng

Ku same mu a https://www.facebook.com/naijcomhausa

Ko a http://twitter.com/naijcomhausa

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Asali: Legit.ng

Authors:
Muhammad Malumfashi avatar

Muhammad Malumfashi (Hausa writer) M. Malumfashi ya samu Digirin farko a ilmin komfuta a ABU Zaria. Baya ga haka ya yi Digirgir a fannin kula da bayanai da wani Digirgir a ilmin aikin jarida duk daga jami'ar. Malumfashi ya kan kawo labaran siyasa, addini, wasanni da al’ada. Ya halarci taron karawa juna sani iri-iri. Imel: muhammad.malumfashi@corp.legit.ng