Tazarce: Buhari ya tseratar da jam’iyyar APC daga mummunan rikici – Sanata Shehu Sani
Sanatan Kaduna ta tskiya, Sanata Shehu Sani ya jinjina ma shugaban kasa Muhammadu Buhari game da matakin tazarcen wa’adin mulki na shuwagabannin jam’iyyar APC daya dauka, inji rahoton gidan Talabijin na Channels.
Sani ya bayyana haka ne cikin wata tattaunawa da yayi da talabijin din, inda yace Buhari ya taimaki APC kwarai da gaske, kuma ya tseratar da jam’iyyar daga fadawa dambarwar siyasa.
KU KARANTA: An yanka ta tashi: Sanatoci sun amshi dala 50,000 don goyon bayan Buhari a rikicin sauya jadawalin zabe
A kwanakin baya ne dai majalisar koli ta jam’iyyar APC ta dauki matakin kara ma shuwagabannin jam’iyyar APC wa’adin mulki na tsawon shekara guda daya, tun daga mazabu har zuwa matakin kasa gaba daya, sai dai matakin bai dace tsarin mulkin jam’iyyar ba, inji Buhari.
Majiyar Legit.ng ta ruwaito shi yana cewa: “Da Buhari bai shiga cikin rikicin ba, da jam’iyyar ta samu kanta cikin mawuyacin hali, don haka na ji dadin wannan mataki sosai, idan da ace an cigaba da wannan tsari, da yan adawa sun yi ta kwace kujerun mu ta hanyar zuwa Kotu, saboda bamu da halastaccen shugabanci.”
Sai dai Sanatan yace akwai wasu yan siyasa dake yi ma Buhari ingiza mai kan turuwa, don biyan wata bukata ta kashin kansu. “Na fada ma Buhari gaba da gaba cewa kada ya amince a wannan matakin tsawaita wa’adin mulkin shuwagabannin jam’iyyar, don kuwa mu yayan jam’iyyar bama goyon baya.”
Ku biyo mu a https://www.facebook.com/naijcomhausa
ko a http://twitter.com/naijcomhausa
Ga masu shawara ko korafi, a same mu a labaranhausa@corp.legit.ng
Asali: Legit.ng