Boko Haram: Majalisar dinkin duniya ta zuba N4n domin ceto rayuka a Arewa maso gabas

Boko Haram: Majalisar dinkin duniya ta zuba N4n domin ceto rayuka a Arewa maso gabas

Majalisar Dinkin Duniya tace ta tura kimanin naira biliyan hudu domin taimakawa yan gudun hijira 60,000 a Borno da sauran sansanonin gudun hijira a arewa maso gabashin Najeriya.

Ofishin masu kula da harkokin yan gudun hijira na Majalisar Dinkin Duniya, sunce zaa yi amfani da kimanin naira biliyan 3.2 wajen samar da gayan agaji ga wasu yan gudun hijira 60,000 a wannan rikici na Boko Haram dake faruwa a Borno.

Hukumar bayar da taimako na Majalisar Dinkin Duniyan sun yi bayanin cewa an tura kudin ne daga asusun taimako na UN.

Boko Haram: Majalisar Dinkin Duniya ta zuba N4n domin ceto rayuka a Arewa maso gabas
Boko Haram: Majalisar Dinkin Duniya ta zuba N4n domin ceto rayuka a Arewa maso gabas

KU KARANTA KUMA: Allah ya isa ga masu amfani da sunana a shafukan yanar gizo suna bata mun suna - Maryam Booth

Majalisar Dinkin Duniyan tayi bayanin cewa rikicin day an ta’addan Boko Haram keyi wanda yaki ci yaki cinyewa na daya daga cikin mafi girman rikici a duniya.

A baya Legit.ng ta tattaro cewa gobara ya kwace a sansanin yan gudun hijra da ke karamar hukumar Rann Kalabage na jihar Borno.

Idan ka na da wata shawara ko bukatar ba mu labari, a tuntube mu a labaranhausa@corp.legit.ng

Ku same mu a https://www.facebook.com/naijcomhausa Ko a http://twitter.com/naijcomhausa

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Asali: Legit.ng

Authors:
Mudathir Ishaq avatar

Mudathir Ishaq Mudathir Ishaq is the head of the Hausa desk at Legit.ng. He studied Industrial Chemistry as first degree at the University of Abuja, Journalism (CSR Specialization) with the Michigan State University and runs MSc Industrial Chemistry from the Nasarawa State University, Keffi. With more than a decade experience in news reporting and content editing, he has interviewed influential personalities. He can be reached on: mudathir.ishaq@corp.legit.ng