Pate: Ministan Tinubu Ya Fadi abin da Ya Hana Shi Neman Takarar Gwamnan Bauchi
- Ministan lafiya da walwalar jama’a, Farfesa Ali Pate, ya sanar da cewa ba zai tsaya takarar Gwamnan jihar Bauchi ba a zaɓen 2027
- Pate ya bayyana cewa ya yanke wannan shawarar ne domin ya ba da fifiko wajen yi wa ƙasar Najeriya hidima a matakin tarayya
- Duk da matsin lamba daga al’ummar Bauchi, ministan ya ce akwai hanyoyi da dama na kawo ci gaba ba tare da mutum ya riƙe muƙami ba
Sani Hamza ƙwararren edita ne a fannin nishaɗi, al'amuran yau da kullum, da kuma siyasa, wanda ke da shekaru sama da biyar a aikin jarida.
Bauchi – Ministan lafiya, Farfesa Ali Pate, ya fayyace dalilansa na janye jiki daga takarar gwamnan jihar Bauchi a babban zaɓen shekarar 2027 mai zuwa.
A cikin wani saƙon bidiyo da aka yaɗa a ranar Lahadi, Pate ya amince cewa ya samu kira daga sassa daban-daban na jihar Bauchi da suke roƙonsa ya fito takara.

Source: Twitter
Dalilin Ali Pate na kin fitowa takara
Jaridar Punch ta ruwato ministan ya bayyana wa al'ummar Bauchi da ma Najeriya baki daya cewa:
“Ina sane da kiran da mutanenmu suke yi a kowane lungu da saƙo na in shiga takarar, amma wannan lokaci ne da ake buƙatar hidimata a tarayya fiye da jihar Bauchi.”
Wannan mataki ya biyo bayan tuntuɓar juna da ya yi da dattawa, matasa, da sauran masu ruwa da tsaki, inda ya ga dacewar ci gaba da ba da gudunmawa ga gwamnatin tarayya domin sake gina ƙasa.
Ali Pate ya jaddada cewa Najeriya tana buƙatar gudunmawar kowane ɗan ƙasa a halin yanzu domin shawo kan ƙalubalen da ake fuskanta.
Ya bayyana cewa mutum na iya taimaka wa ci gaban ƙasa ta hanyoyi da dama, ba lallai sai ta hanyar riƙe muƙamin gwamna a matakin jiha ba.
Matsayar Ali Pate kan siyasar 2027
Duk da cewa ba zai tsaya takara ba, Ali Pate ya lashi takobin ci gaba da gudanar da harkokin siyasa ta hanyar mara wa ƴan takara na gari baya.
Ya bayyana cewa zai tabbatar da cewa mutanen da zai goyi baya su ne waɗanda suke da gaskiya da riƙon amana, ba waɗanda ke bayyana lokacin zaɓe kawai ba.
Pate ya yi kira ga al'umma da su ba wa gwamnatin Bola Tinubu da jam'iyyar APC goyon baya domin samun haɗin kai tsakanin tarayya da jiha.
Ya ƙara da cewa daidaito tsakanin gwamnatin jiha da ta tarayya shi ne zai samar da ingantaccen ci gaba ga al'ummar jihar Bauchi.

Source: Original
Sakon gargadi ga matasan Bauchi
Ministan ya yi amfani da wannan dama wajen jan kunnen matasa da su guji zama makaman yaƙi a hannun ƴan siyasa masu son zuciya.
Ya buƙaci matasa da su nisanci shaye-shayen miyagun ƙwayoyi, tashin hankali, da kuma siyasar rarraba kai wadda ba ta haifar da ɗa mai ido.
“Matasa ba shugabannin gobe ba ne kawai, su ne shugabannin yau. Dole ne su guji duk wanda ke neman raba kansu ko amfani da su wajen tashin hankali.”
- Farfesa Ali Pate.
Kalli bidiyon bayanin Ali Pate a kasa, wanda shafin Labari Daga Bauchi ya wallafa a Facebook:
Matsayin Ali Pate a fannin kiwon lafiya
A wani labari, mun ruwaito cewa, Ministan Lafiya, Farfesa Ali Pate, ya samu yabo daga masana, bayan an saka shi cikin jerin manyan mutane 100 a fannin lafiya a duniya.
Kungiyar GHC ta yaba da rawar da ya taka wajen gyaran fannin lafiya da kokarinsa na bunkasa samar da magunguna a cikin gid.
An kuma bukaci ya warware rikice-rikicen da ke cikin fannin lafiya ta hanyar adalci da mutunta dukkan ma’aikatan lafiya a kasar nan.
Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.
Asali: Legit.ng


