Zanga Zanga Ta Barke a Abuja, Maza da Mata Sun Mamaye Babbar Kotun Tarayya

Zanga Zanga Ta Barke a Abuja, Maza da Mata Sun Mamaye Babbar Kotun Tarayya

  • Wasu gungun maza da mata ƙarƙashin inuwar "masu ruwa da tsaki daga Arewa" sun gudanar da zanga-zanga a babbar kotun tarayya da ke Abuja
  • Masu zanga-zangar sun gargaɗi Shugaba Bola Tinubu da ya daina tsoma baki a harkokin shari'a da kuma hukumar zaɓe mai zaman kanta (INEC)
  • Wannan mataki na zuwa ne yayin da babban lauyan gwamnatin tarayya ta goyi bayan wata kara, wacce ke neman soke rajistar wasu jam'iyyun siyasa

Sani Hamza ƙwararren edita ne a fannin nishaɗi, al'amuran yau da kullum, da kuma siyasa, wanda ke da shekaru sama da biyar a aikin jarida.

Abuja – Yanayi ya ɗanyi zafi a ranar Litinin a harabar babbar kotun tarayya da ke Wuse, Abuja, yayin da ɗimbin masu zanga-zanga suka mamaye ƙofar shiga kotun.

Masu zanga-zangar sun riƙa rera waƙoƙin neman adalci tare da ɗaga kwalaye masu rubuce-rubucen kira ga Shugaba Bola Tinubu da ya bar dimokuradiyya ta numfasa.

Kara karanta wannan

Bayan an yi masa tayin takara, shugabannin NDC sun gana da Kwankwaso a gidansa

Masu zanga zanga sun mamaye babbar kotun tarayya Abuja.
Gungun masu zanga zanga maza da mata a babbar kotun tarayya da ke Abuja. Hoto: UGC
Source: UGC

Zanga zanga ta barke a Abuja

Jami’an tsaro, ciki har da na farin kaya (DSS), sun tare hanyar shiga kotun domin hana masu zanga-zangar shiga cikin harabar kotun, in ji rahoton The Punch.

Shugaban gungun masu zanga-zangar, Banki Sharrif, ya bayyana cewa akwai babbar barazana ga ƴancin fannin shari'a da kuma cibiyoyin dimokuradiyya a ƙasar nan.

Sharrif ya bayyana cewa:

“Muna kira ga Shugaba Bola Ahmed Tinubu da ya dakatar da kowane nau'i na tsoma baki, na fili ko na ɓoye, a fannin shari'a. Bai kamata a mayar da kotuna kayan aikin siyasa ba."

Kare jam’iyyun adawa da dimokuradiyya

Masu zanga-zangar sun bayyana cewa duk gwamnatin da ke ƙoƙarin raunata ƴan adawa, to ba ta yarda da kanta ba, kuma tana jin tsoron matakin 'yan kasa ne.

Sun jaddada cewa dimokuradiyya tana bunƙasa ne kawai idan akwai gasa ta gaskiya, inda suka gargaɗi gwamnati kan amfani da dabarun shari'a domin soke rajistar jam'iyyun siyasa, musamman waɗanda ke da ƙarfi a Arewacin Najeriya.

Kara karanta wannan

Kano: Shugaban ƙaramar hukuma ya ba da mamaki, ya raba wa mata tallafin 'omo'

Sun bayyana cewa zaɓen da babu ƴan adawa masu ƙarfi, wasan kwaikwayo ne kawai.

Wannan matsin lamba ya biyo bayan ƙoƙarin da ake zargin ana yi na soke rajistar wasu jam'iyyun siyasa ta hanyar amfani da shigar da kararraki a kotu.

An gargadi babban lauyan tarayya

Masu zanga-zangar sun yi kira ga babban lauyan gwamnati, Lateef Fagbemi, da ya kasance mai bin doka da oda, in ji rahoton shafin Politics Nigeria.

Sun gargaɗi Fagbemi kan mayar da ofishinsa makamin yaƙin siyasa ga gwamnati mai ci yayin da suka bayyana cewa idan ƴan ƙasa suka rasa aminci da kotuna, za su koma neman adalci a kan titi, wanda hakan barazana ne ga zaman lafiyar ƙasa.

Masu zanga-zangar sun lashi takobin ci gaba da sanya ido kan duk wani mataki da gwamnatin Tinubu ko kotuna za su ɗauka a nan gaba.

Masu zanga zangar sun dura babbar kotun tarayya ne don nuna adawa da shirin soke rajistar jam'iyyun adawa
Harabar babbar kotun tarayya da ke Abuja inda mutane ke zanga zanga. Hoto: Light Oriye Tamunotonye/AFP
Source: Getty Images

sDalilin fusatar masu zanga zangar

Babban abin da ya haifar da wannan zanga-zanga shi ne wata ƙara da babban lauyan gwamnati ya goya wa baya, wacce ke neman soke rajistar wasu jam'iyyun siyasa da dama.

Kara karanta wannan

2027: Shugaba Tinubu ya karbi fom din neman sake tsayawa takara a inuwar APC

Wannan ya sa ƴan adawa da dama fargabar cewa ana neman ruguza tsarin jam'iyyu da dama a Najeriya domin share wa jam'iyyar APC fage don lashe zaɓen 2027.

An je kotu neman soke rajistar jam'iyyu

A wani labarin, mun ruwaito cewa, babban lauyan gwamnatin tarayya kuma Ministan shari'a, Lateef Fagbemi yana kotu domin soke rajistar wasu jam'iyyun siyasa.

Daga cikin jam'iyyun da ake so a soke akwai babbar jam'iyyar adawa ta ADC da ta sha alwashin kifar da Bola Tinubu a zaben 2027.

Lateef Fagbemi ya bayyana cewa jam'iyyun da ake nema hukumar zabe ta kasa (INEC) ta soke su ba su cika ka'idar rajista ba a Najeriya.

Asali: Legit.ng

Authors:
Sani Hamza avatar

Sani Hamza (Hausa Editor) Sani Hamza ma'aikaci ne da ya yake da gogewa a aikin jarida. Ba fassara labarai da wallafasu a yanar gizo kadai ba, Sani yana da kwarewa a aikin rediyo da talabijin. Ya kuma shafe shekaru 8 a masana'antar fina-finai da dab'i. Imel: sanihamzafuntua@gmail.com