APC ko ADC: Gwamna Makinde Ya Bayyana Jam'iyyar da Za Ta Samar da Shugaban Kasa a 2027

APC ko ADC: Gwamna Makinde Ya Bayyana Jam'iyyar da Za Ta Samar da Shugaban Kasa a 2027

  • Gwamnan jihar Oyo, Seyi Makinde, ya yi hasashen abin da zai faru a zaben shugaban kasa na shekarar 2027 da ake tunkara
  • Injiniya Seyi Makinde ya bayyana cewa jam'iyyarsa ta PDP za ta lashe kujeru a matakai daban-daban ciki har da shugaban kasa
  • Gwamnan ya kuma bukaci mambobin jam'iyyar PDP da su hada kansu tare da fara shiri domin tunkarar babban zaben 2027

​​​​​​​​​​​​​​​​Editan Legit Hausa Sharif Lawal yana da kwarewar shekaru wajen kawo rahotannin siyasa, al'amuran yau da kullum, tsegumi da nishadi

FCT, Abuja - Gwamnan jihar Oyo, Seyi Makinde, ya yi magana kan zaben shugaban kasa na shekarar 2027 da ake tunkara.

Gwamna Seyi Makinde ya bayyana kwarin gwiwar cewa jam’iyyar PDP ce za ta samar da shugaban ƙasar Najeriya na gaba a babban zaɓen 2027.

Seyi Makinde ya hango nasarar PDP a 2027
Gwamna Seyi Makinde na jihar Oyo Hoto: Seyi Makinde
Source: Twitter

Jaridar Vanguard ta kawo rahoton cewa Gwamna Makinde ya yi wannan ikirarin ne ranar Litinin, 4 ga watan Mayun 2026.

Kara karanta wannan

Tsohon shugaban kasa, Jonathan ya canza jam'iyya don ya fito takara a 2027? Gaskiya ta bayyana

Makinde ya yi ikirarin ne yayin da yake jawabi ga mambobin jam’iyyar da masu ruwa da tsaki a taron kwamitin zartarwa na kasa (NEC) karo na 103 na wani ɓangaren jam’iyyar PDP da aka gudanar a Abuja.

Me Seyi Makinde ya ce kan PDP?

Yayin da yake jawabi a wurin taron, Gwamna Makinde ya ce jam’iyyar tana nan daram wajen ganin ta ƙwace mulki a dukkan matakai, inda ya buƙaci mambobi da su kasance cikin haɗin kai tare da mayar da hankali gabanin zaɓubbukan, jaridar The Punch ta kawo labarin.

“Ya kamata mu rubuta hakan mu ajiye. Wannan taron zai samar da mambobin majalisar dokoki ta jiha, zai samar da mambobin majalisar wakilai, zai samar da sanatoci, zai samar da Gwamnoni sannan zai samar da shugaban kasa na gaba."

- Gwamna Seyi Makinde

PDP ta nada kwamitin rikon kwarya

Taron ya kuma amince da naɗin kwamitin riƙon kwarya mai mambobi 13 domin gudanar da harkokin wannan ɓangare na jam’iyyar.

Tanimu Turaki ne ke jagorantar kwamitin, yayin da Taofeek Arapaja zai kasance sakataren kwamitin na kasa.

Wannan matakin ya biyo bayan wani kuduri da Tony Aziegbemi ya gabatar, sannan Clement Fagboyede ya goyi bayansa.

Kara karanta wannan

"Mu kece raini": Gwamnan Gombe ya yi martani bayan kafiyar Pantami da Goje

Seyi Makinde ya yi magana kan PDP
Gwamnan jihar Oyo, Seyi Makinde Hoto: Seyi Makinde
Source: Facebook

Sauran mambobin kwamitin sun haɗa da Daniel Ambrose, Hamza Abuya, Ihediwa, Isah Abubakar, Theophilus Dakashan, Ini Ememobong, Aribisala Adewale Idowu, Baru Shaffi, da kuma Okechukwu Obiechina.

Wannan ci gaba na zuwa ne a daidai lokacin da ake ci gaba da sauya fasalin cikin gida a jam’iyyar PDP, yayin da shugabannin jam’iyyar ke ci gaba da tuntuɓar juna da ƙoƙarin sake tsarin jam’iyyar gabanin babban zaɓen 2027.

Wani mamban PDP a Katsina, Ibrahim Sanusi, ya nuna shakku kan kalaman da gwamnan na jihar Oyo kan samun nasarar jam'iyyar.

"Ba boyayyen abu ba ne cewa jam'iyyar mu na fama da rikicin cikin gida da na shugabanci. A yadda abubuwa suke tafiya a yanzu babu yadda za a yi mu iya samun nasarar lashe zaben shugaban kasa."
"Jam'iyyar da ta ke fama da rarrabuwar kai ba yadda za a yi ta samu nasara idan ta shiga zabe a haka."

- Ibrahim Sanusi

Kara karanta wannan

ADC: Tsohon minista, Amaechi ya zama na 2 da ya sayi fam na takarar shugaban kasa a 2027

Gwamna Bala ya fice daga jam'iyyar PDP

A wani labarin kuma, kun ji cewa Gwamnan jihar Bauchi, Sanata Bala Mohammed, ya sanar da ficewarsa daga jam'iyyar PDP mai adawa a Najeriya.

Gwamna Bala Mohammed, ya sanar da sauya shekar sa daga jam’iyyar PDP zuwa Allied Peoples Movement, wato APM.

Majiyoyi suka ce gwamnan ya fice ne tare da magoya bayansa masu biyayya ga bangaren Tanimu Turaki kwanaki biyu bayan hukuncin Kotun Koli kan rikicin shugabanci.

Asali: Legit.ng

Authors:
Sharif Lawal avatar

Sharif Lawal (Hausa Editor) Sharif Lawal ma'aikacin jarida ne wanda ya samu gogewa a harkar aikin jarida. Ya yi digirinsa na farko a jami'ar Ahmadu Bello (ABU) da ke Zaria. Ya samu horo daga Reuters kan aikin jarida da tantance labarai. Za a iya tuntubarsa ta Sharif.lawal@corp.legit.ng