Latest
Jaridar Daily Nigerian ta samu rahoton cewa gwamnan jihar Kano, Abdullahi Umar Ganduje, ya zabi kwamishanan aikin noma, Nasiru Gawuna, a matsayin mataimakin gwamnan jihar. Kimanin wata daya kenan da Ganduje ke shugabancin jihar ba
Dahiru Bauchi da mutanen sa sun gana da Buhari. Babban Malami Dahiru Bauchi ya ziyarci Shugaban Najeriya Muhammadu Buhari ne a fadar Shugaban kasa. Mun samu hotunan zaman ne daga Buhari Sallau wanda yake kusa da Shugaban kasa.
Mun ji cewa Yusuf Lassun ya bi Dogara ya koma PDP ma'ana dai yanzu haka dai APC ba ta rike da shugabancin Majalisar Kasar duk da cewa ita ta kafa Gwamnati bayan Shugaban Majalisar Dattawa Bukola Saraki ya bar APC kwanaki.
Kokomba na matukar taimakawa jiki ta hanyoyi da dama, kamar taimakon idanu da kuma sinadaran dake taimakawa wajen narkar da abinci. Kazalika tana dauke da sinadarai masu yawa da jiki ke bukata a kullum. Citta ma na taka muhimmiyar
Za ku ji ashe Jonathan na sa rai Jam’iyyar PDP ta lashe zaben 2019 a Najeriya yace Sule Lamido ya cancanci mulkin kasar nan. A cewar Jonathan, kan mutanen Najeriya ya rabu matuka a wannan lokaci na Gwamnatin Buhari.
Gwamnan Legas Ambode ya nemi Tinubu ya yafe masa zunuban sa bayan ya ji cewa Bola Tinubu wanda jigo ne a siyasar Yarbawa da kuma mutanen sa na yunkurin kakaba Mista Jide Sanwo-Olu a matsayin Gwamna a Jam’iyyar APC a zaben 2019.
An kama wani ‘Dan Najeriya da ya hana Turawa sakat da 419. ‘Yan sandan Australia ne su ka kama wani dan Najeriya da ke damfara daga cikin cibiyar tsaro ta shige da fice a birnin Sydney. An ce wannan mutumin yana da shekara 43.
Rikicin da ake fama da shi na cikin gida a Jam’iyyar APC Adamawa na cigaba da yin gaba. Yanzu dai har ta kai Jam’iyyar APC a Adamawa tayi watsi da Surukin Shugaban kasa Buhari ta zabi Gwamna a matsayin ‘Dan takarar 2019.
Za ku ji cewa Gwamna Okorocha ya nada sabon SSG a Jihar Imo. Rochas Okorocha zai nada kwamishinoni kusan 7 kwanan nan bayan ya kori wasu 13. Kwanakin ‘Yar uwar sa Gwamnan ta zama Kwamishina lokacin da nada sababbin mukamai.
Masu zafi
Samu kari