Janar Ahmad Vahidi: Kwamadan Iran Mai Zafi da Ya Hana Trump Sakat
- Bayan kashe wasu daga cikin jagororin Iran ciki har da Ayatollah Ali Khamenei, kasar ta maye gurbinsu da wasu shugabanni masu tsauri sosai
- An bayyana cewa Janar Ahmad Vahidi yana da tasiri sosai wajen tafiyar da Iran kuma yana kawo cikas ga shugaban Amurka, Donald Trump
- Wasu rahotanni sun nuna cewa Janar Vahidi yana da karfin fada a ji a kasar Iran a yanzu, ta inda aka ce shi ya jawo nada Mojtaba Khamenei
Editan Legit Hausa Ibrahim Yusuf yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum.
Iran - Bayan hare-haren sama na hadin gwiwar Amurka da Isra’ila sun kashe wasu shugabannin Iran ciki har da manyan jami’ai da dama kasar ta yi sauye-sauye.
Masana sun ce kwamandan rundunar IRGC, Manjo Janar Ahmad Vahidi, ya tattara kusoshin kasar domin karbe iko kan soji da kuma tawagar tattaunawar Iran.

Source: Getty Images
New York Post ta wallafa cewa a lokacin da Vahidi mai shekaru 67 da abokan aikinsa suka karbe iko, Iran ta kara tsaurara matsayarta.
Iran da jami’anta sun ki shiga tattaunawar sulhu da Amurka a wannan mako, tare da kara kai hare-hare kan jiragen ruwa da ke kokarin wucewa ta mashigar Hormuz.
Ana sanya wa Vahidi takunkumi mai tsauri daga kasashen yamma kuma ana kallonsa a matsayin mafi tsauri a Iran wanda ya kawar da masu sassauci, ciki har da wadanda ke jagorantar tattaunawar da Amurka.
Wanene Ahmad Vahidi a Iran?
Vahidi ya taba zama kwamandan rundunar Quds a shekarun 1990, inda ya taimaka wajen fadada tasirin Iran a Gabas ta Tsakiya kafin ya mika jagoranci ga Qasem Soleimani.
Shi da Soleimani ana danganta su da kafa tubalin kungiyoyin da Iran ke marawa baya a kasashen waje, ciki har da kungiyar Hezbollah a Lebanon.
Ba kamar shugabannin IRGC biyu da suka gabata ba, Vahidi ya rike mukamai a siyasa, inda ya taba zama Ministan tsaro da kuma Ministan harkokin cikin gida a gwamnatoci biyu.
Fox News ta wallafa cewa an nada shi Mataimakin shugaban IRGC a watan Disamban 2025 ta hannun marigayi jagoran Iran, Ali Khamenei.
Bayan mutuwar Khamenei da tsohon shugaban IRGC Mohammad Pakpour a hare-haren Amurka da Isra’ila na ranar 28 ga Fabrairun 2026, Vahidi ya zama babban mai iko a rundunar.
Wane ne ke da iko a Iran a yanzu?
Bayan mutuwar Khamenei, Vahidi ya goyi bayan dansa Mojtaba Khamenei ya gaje shi, duk da rahotannin cewa mahaifinsa bai so hakan ba.
Sai dai da Mojtaba ya ji rauni a hare-haren 28 ga Fabrairu kuma bai fito fili ba, masana na ganin sabon jagoran ba shi da cikakken iko, illa kawai ana amfani da shi.

Source: Getty Images
Masani Khosro Isfahani ya ce idan Mojtaba yana raye, to ana amfani da shi ne kawai, ba shi da tasiri a harkokin yanke shawara, kuma gwamnati na iya jingina masa kalamai.
Iran ta kwace wasu jiragen ruwa
A wani labarin, mun kawo muku cewa rundunar sojin kasar Iran ta tabbatar da kwace wasu jiragen ruwa da suka so wucewa ta mashigar Hormuz.
Rundunar ta fitar da wani bidiyo da ya nuna sojojin Iran na fita a wani jirgin yaki suna tunkarar jiragen ruwa suna karkatar da su a teku.
Gwamnatin shugaba Donald Trump ta sanar da cewa kwace jiragen bai karya sharadin tsagaita wuta da suka yi ba domin jiragen ba nata ba ne.
Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.
Asali: Legit.ng


