'Yan Bindiga Sun Farmaki Fadar Basarake yayin Harin Ramuwar Gayya a Zamfara

'Yan Bindiga Sun Farmaki Fadar Basarake yayin Harin Ramuwar Gayya a Zamfara

  • 'Yan bindiga dauke da makamai sun kai harin ta'addanci a jihar Zamfara da ke yankin Arewa maso Yamma na Najeriya
  • Tsagerun 'yan bindigan sun kai hari ne domin ramuwar gayya bayan da dakarun sojoji suka kai farmaki a sansaninsu
  • 'Yan bindigan sun yi barna a harin da suka kai, inda suka kwashe kayayyaki masu daraja tare da kona fadar Hakimin yankin

​​​​Editan Legit Hausa Sharif Lawal yana da kwarewar shekaru wajen kawo rahotannin siyasa, al'amuran yau da kullum, tsegumi da nishadi

Jihar Zamfara - Hankulan jama'a sun tashi bayan wasu ‘yan bindiga dauke da makamai sun kai harin ramuwar gayya a jihar Zamfara.

Tsagarun 'yan bindigan sun kai harin ramuwar gayyar ne a ƙauyen Yankuzo da ke ƙaramar hukumar Tsafe a jihar Zamfara.

'Yan bindiga sun kai hari a Zamfara
Gwamnan jihar Zamfara, Dauda Lawal Hoto: Dauda Lawal
Source: Facebook

Jaridar Leadership Hausa ta kawo rahoton cewa 'yan bindiga sun kona fadar Hakimin yankin, Alhaji Babangida Hamza, yayin farmakin da suka kawo.

Kara karanta wannan

'Yan ta'adda sun kutsa asibiti a Neja, babban likita ya fada hannun miyagu

'Yan bindiga sun yi ta'asa a Zamfara

Hakazalika, 'yan bindigan sun sace kayayyaki masu daraja a harin na ta'addanci da suka kai a kauyen.

Rahoton jaridar Premium Times ya nuna cewa 'yan bindigan sun kawo harin ne bayan wani artabu da suka yi da sojoji na tsawon sa’o’i uku sakamakon harin da aka kai maɓoyarsu a yankin.

Rahotanni sun ce maharan, ƙarƙashin jagorancin wani da ake kira da suna Mai Rasha, sun mamaye ƙauyen a ranar Talata, 21 ga watan Afirilun 2026.

'Yan bindiga sun kona fadar Hakimi

'Yan bindigan wadanda suke dauke da makamai sun rika harbi kan mai uwa da wabi, kafin daga bisani su cinna wuta a fadar Hakimin.

Alhaji Babangida Hamza ya bayyana cewa lokacin da 'yan bindigan suka kawo harin yana garin Tsafe.

“Sun shigo suna harbi kai tsaye suka nufi fadata suka ƙona ta."

- Alhaji Babangida Hamza

Hakimin ya kara da cewa, an samu nasarar kwashe iyalansa zuwa wurin da yake da tsaro, amma har zuwa yammacin ranar Laraba, 22 ga watan Afirilun 2026, ba a tantance yawan waɗanda suka mutu ko suka jikkata ba.

Kara karanta wannan

Ba sauki: Sojoji sun kashe babban kwamandan ISWAP da 'yan ta'adda da dama

'Yan bindiga sun kona fadar Hakimi a Zamfara
Taswirar jihar Zamfara, tarayyar Najeriya Hoto: Legit.ng
Source: Original

'Yan bindiga sun tafka sata

Mutanen yankin sun ce 'yan bindigan sun shafe sa’o’i da dama a ƙauyen suna ta'asar su har zuwa misalin ƙarfe 3:30 na rana.

'Yan bindigan sun rika kwasar kayan abinci da sauran kayayyaki masu daraja daga shaguna daban-daban a yayin harin da suka kawo.

Hakimin yankin ya bayyana cewa harin na ramuwar gayya ne sakamakon farmakin da dakarun sojojin da suka kai a sansanonin ‘yan ta’adda dake kusa da yankin a daren ranar.

'Yan ta'adda sun sace likita a Neja

A wani labarin kuma, kun ji cewa wasu 'yan ta'adda dauke da makamai sun yi shigar bazata a wani asibiti da ke jihar Neja.

'Yan ta'addan sun yi garkuwa da wani likita mai suna Anthony Enahoro, a gundumar Wawa da ke ƙaramar hukumar Borgu a jihar Neja.

Mutanen yankin suna zargin cewa an sace likitan ne domin ya ba da magani ga mayakan da suka ji rauni ko kuma waɗanda ba su da lafiya.

Asali: Legit.ng

Authors:
Sharif Lawal avatar

Sharif Lawal (Hausa Editor) Sharif Lawal ma'aikacin jarida ne wanda ya samu gogewa a harkar aikin jarida. Ya yi digirinsa na farko a jami'ar Ahmadu Bello (ABU) da ke Zaria. Ya samu horo daga Reuters kan aikin jarida da tantance labarai. Za a iya tuntubarsa ta Sharif.lawal@corp.legit.ng