An Kai wa Dan Tsohon Sarkin Iran Mai Goyon Bayan Trump Hari
- Dan tsohon Sarkin Iran da aka kifar da gwamnatinsa a 1979, Reza Pahlavi ya gamu da wani mummunan lamari yayin da ya je taro a Jamus
- Wani mutum ya kutsa wajen da Reza Pahlavi ke tafiya ya fesa masa ruwan tumatur a wuya, lamarin da ya jawo ce-ce-ku-ce a fadin duniya
- Reza Pahlavi ya sha nuna kan shi a matsayin wanda ya kamata a ce yana mulkin Iran a yanzu kuma yana goyon bayan hare-haren Amurka
Editan Legit Hausa Ibrahim Yusuf yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum.
Germany - An kai wa Yariman Iran da ke gudun hijira, Reza Pahlavi hari da ruwan tumatir yayin da yake fita daga wani taron manema labarai inda ya soki yarjejeniyar tsagaita wuta tsakanin Amurka da Tehran.
Bidiyon lamarin ya nuna wani ruwa ja yana sauka a bayan wuyansa da rigar shi yayin da yake barin wurin taron a birnin Berlin a ranar Alhamis.

Source: Getty Images
Rahoton Telegraph ya nuna cewa ‘yan sanda sun kama mutumin da ya jefa wa Reza Pahlavi ruwan tumatur nan take ai dai ba a tabbatar ba ko yana goyon bayan gwamnatin Tehran ba.
Bayanin 'yan sanda kan harin
Kakakin ‘yan sanda ya ce fasa wa Pahlavi wani jan ruwa yayin da ya ke tafiya, wanda ake ganin ruwan tumatir ne, inda ya ce bai ji rauni ba.
Ya ce wanda ake zargin ba a taba samun ya shiga hannun jami’an tsaro ba, amma ana ci gaba da bincike kan zargin neman haddasa rauni, lalata dukiya da kuma cin zarafi game da shi.
Wasu rahotanni sun nuna cewa an sanar da cewa:
“Yariman bai ji rauni ba kuma ya ci gaba da shirye-shiryensa a Berlin kamar yadda aka tsara.
“Yariman na son a mayar da hankali kan halin da al’ummar Iran ke ciki, wadanda ke fuskantar hukuncin kisa, kashe-kashe, azabtarwa da fyade a kullum. Ya kuma gode wa ‘yan sandan Berlin bisa goyon bayansu.”

Kara karanta wannan
Hormuz: Matakin Amurka da Iran ya ta'azzara farashin fetur a duniya, ganga ta haura $100
Rahotanni sun nuna cewa akwai kusan mutane 300,000 ‘yan asalin Iran da ke zaune a Jamus, wanda shi ne mafi yawa a tarayyar Turai.
Wane ne Reza Pahlavi a Iran?
Pahlavi dan Mohammad Reza Pahlavi ne, tsohon Sarkin Iran wanda ya mulki kasar daga 1941 har zuwa 1979 lokacin da aka kifar da shi, lamarin da ya haifar da kafuwar Jamhuriyar Musulunci.

Source: Getty Images
Duk da kasancewarsa a gudun hijira tsawon rayuwarsa, Pahlavi yana kokarin gabatar da kansa a matsayin jagoran Iran, inda yake haduwa da jami’an gwamnati, magoya baya da kafafen yada labarai.
Ga bidiyon ki masa hari da Al Jazeera ta wallafa a X:
Iran: Janar Vahidi ya addabi Trump
A wani labarin, mun kawo muku cewa Janar Ahmad Vahidi ya kasance daya daga cikin kwamandojin rundunar sojin Iran mai zafi a halin yanzu.
Kasancewar ya shafe shekaru yana aikin soja da kuma rike mukamai da dama, Vahidi ya zama mai tasiri sosai a Iran bayan kashe shugabanninta.
An bayyana shi a matsayin wanda ke kawo wa shugaba Donald Trump cikas game da abubuwan da yake son cimmawa a Iran bayan fara yaki.
Asali: Legit.ng
