Rochas Okorocha yayi sababbin nade-naden mukamai a Jihar Imo

Rochas Okorocha yayi sababbin nade-naden mukamai a Jihar Imo

Jiya mu ka ji cewa Gwamnan Jihar Imo Rochas Okorocha ya nada sabon Sakataren Gwamnatin Jiha watau SSG bayan tsige Surukin sa Uche Nwosu da wasu manyan mukarraban sa har 16 a makon jiya.

Rochas Okorocha yayi sababbin nade-naden mukamai a Jihar Imo
Gwamna Okorocha ya nada sabon SSG a Jihar Imo
Asali: UGC

Rochas Anayo Okorocha ya nada Cif Mark Uchendu a matsayin sabon Sakataren Gwamnatin Jihar Imo. Bayan nan kuma Gwamnan na Imo ya nada Messrs Kenneth Chid Ejiogu a matsayin Shugaban Ma’aikatar fadar sa.

Bayan nan kuma Gwamnan ya nada Chukwuemeka Valentine Duru a matsayin sabon babban Sakataren Gwamnan. Haka kuma Victor Nwanaforo Onyechere ya zama Mataimakin Shugaban Ma’aikatar fadar Gwamnan na APC.

KU KARANTA: Ministoci 3 a Gwamnatin Buhari da su kayi murabus

Mai Girma Gwamnan ya zabi mutum 7 a wadanda za a tantance a matsayin Kwamishinoni. Gwamnan dai zai aika sunayen: Bonaventure Akwiwu, Sunny Chiadi. Esther Egburuche, Patrick Nze, Chinyere Uwandu, Mr. Kelechi Azike.

Haka kuma akwai Edna Okorie da Injiniya Chika Ezeji da za tura sunayen su zuwa Majalisa. Za a tabbatar da wadanda aka ba mukaman ne a Ranar Litinin dinnan inji Sakataren gidan Gwamnatin Jihar watau Sam Onwuemeodo.

A cikin nade-naden da Gwamna Okorocha yayi akwai Ijeoma Igboanusi wanda ta na cikin manyan Mukarrabai a fadar sa. A baya dai Gwamnan ya taba ba wata ‘Yar uwar sa irin wannan mukami.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku same mu a https://www.facebook.com/naijcomhausa

Ko a http://twitter.com/naijcomhausa

Idan ka na da wata shawara ko bukatar ba mu labari, a tuntube mu a labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel