Addu'ar lashe zabe: Wasu 'yan Kwankwasiyya sun gudanar da Sallah, saukar al'qur'ani da yanka

Addu'ar lashe zabe: Wasu 'yan Kwankwasiyya sun gudanar da Sallah, saukar al'qur'ani da yanka

- Wasu 'yan Kwankwasiyya sun gudanar da Sallah, saukar al'qur'ani da yanka

- Sun yi hakan ne domin neman agajin Allah ga gwanin su

Yayin da zabukan shekarar 2019 ke ta kara karatowa, wasu masoyan dan takarar shugabancin kasar dake neman tikitin tsayawa a jam'iyyar adawa ta PDP, Dakta Rabi'u Musa Kwankwaso sun yanka rago tare da addu'o'i ga Allah akan muradin na su.

Addu'ar lashe zabe: Wasu 'yan Kwankwasiyya sun gudanar da Sallah, saukar al'qur'ani da yanka
Addu'ar lashe zabe: Wasu 'yan Kwankwasiyya sun gudanar da Sallah, saukar al'qur'ani da yanka
Asali: UGC

KU KARANTA: An kama wani dan majalisa yana wanka tsirara a Najeriya

Kamar yadda muka samu, masoyan na Kwankwaso da galibin su matasa ne sun fito ne daga karamar hukumar Kiru dake a jihar Kano inda kuma suka gudanar da Sallah da saukar al'qur'ani duk domin samun nasarar gwanin nasu.

Legit.ng dai ta samu cewa Kwankwaso dake zaman tsohon gwamnan jihar Kano ya fice daga jam'iyyar sa ta APC zuwa PDP a watannin baya inda kuma ya bayyana kudurin sa na tsayawa takara da Shugaba Buhari a watan da ya gabata.

A wani labarin kuma, Labarin da muke samu daga majiyoyin mu dai na nuni ne da cewa babban jami'in sojan Najeriyar nan watau Manjo Janar Idris Alkali da muka baku labarin bacewar sa a kwanan baya an tsinci gawar sa.

Mun samu cewa dai an tsinci gawar sojan ne a garin Jos ta jihar Filato a kusa da asibitin koyarwa ta jami'ar tarayya dake jihar akan hanyar zuwa matsugunnin jami'ar na din din din.

Latsa wannan domin samun labarai a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/naijcomhausa

Twitter: https://twitter.com/naijcomhausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel