Daga karshe, Ganduje ya nada Gawuna matsayin mataimakin gwamna
Jaridar Daily Nigerian ta samu rahoton cewa gwamnan jihar Kano, Abdullahi Umar Ganduje, ya zabi kwamishanan aikin noma, Nasiru Gawuna, a matsayin mataimakin gwamnan jihar.
Kimanin wata daya kenan da Ganduje ke shugabancin jihar ba tare da mataimaki ba tun lokacin da tsohon mataimakin farfesa Hafiz Abubakar yayi murabus ranan 5 ga watan Agusta.
An zabi Malam Nasiru Gawuna wanda tsohon shugaban karamar hukuma ne kuma shugaban kungiyar wasannin matasan Najeriya cikin mutani hudu da gwamnan ke kokarin zaba.
KU KARANTA: Cikakken tarihin Bajimin Malamin Musulunci Imam Bukhari
Majiyar tace: "An rigaya da tura sunansa majalisar dokokin jihar domin bincike. Ana sa ran rantsar da shi ranan Talata ko Laraba ,"
Gabanin haka, gwamna Ganduje ya mika sunan Nasiru Gawuna a matsayin wanda zai tsaya takara da shi a matsayin mataimakin gwamna a 2019.
Idan ka na da wata shawara ko bukatar ba mu labari, a tuntube mu a labaranhausa@corp.legit.ng Ku same mu a https://www.facebook.com/naijcomhausa Ko a http://twitter.com/naijcomhausa Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en
Asali: Legit.ng