Gwamnan Legas Ambode ya sulale Abuja domin ya ga babban Jigon APC Tinubu
Mun samu labari cewa Gwamna Akinwumi Ambode ya ruga zuwa babban Birnin Tarayya Abuja domin ya gana da Asiwaju Bola Ahmed Tinubu a game da zaben 2019 ganin yadda kujerar sa ta ke rawa.
Ana kishin-kishin din cewa Akinwumi Ambode ya tafi Abuja ne domin ya nemi afuwar Bola Tinubu ya kuma nemi ya dafa masa domin ya zarce a kan kujerar sa. Yanzu dai har Shugaban kasa Buhari ya shiga cikin rikicin na Legas.
Jaridar Punch dai ta rahoto cewa manyan APC sun zauna da Tinubu domin nemawa Gwamnan na Legas afuwa. Mataimakin Shugaban kasa Yemi Osinbajo da kuma Shugaban Jam’iyya Adams Oshiomhole ne su ka gana da Tinubu.
Wata Majiya daga Jaridar dai tace Ambode ya gana da Asiwaju Bola Tinubu a Abuja amma babu wanda ya san yadda zaman ya kasance. Yanu dai kujerar Ambode tana girgidi bayan Tinubu ya jawo Jide Sanwo-Olu ya nemi Gwamna.
KU KARANTA: Babu wata rigima tsakani na Mai gida na Tinubu - Ambode
Gwamnan ya taso ta-ka-nas har ne domin ya ba Mai gidan na sa hakuri inda ake tunani ya fara hakura amma dai babu tabbacin cewa abubuwa sun dawo daidai. Manyan Kasar Yarbawa dai sun sa baki Tinubu ya dagawa Ambode kafa.
Farfesa Yemi Osinbajo da Adams Oshiomhole sun zauna da Bola Tinubu inda su ka roke sa ya guji yin abin da zai kawowa APC cikas a 2019. A Garin Epe dai inda nan ne Ambode ya fito, ana ta yi masa addu’a ya samu nasara a zabe mai zuwa.
Shi kuma yaron Tinubu watau Babajide Olusola Sanwo-Olu wanda ya sha alwashin tika Ambode a Jam’iyyar APC da kasa yace ba zai fasa fitowa neman Gwamna a 2019 ba inda ma ya shiya kaddamar da shirin takarar na sa yau dinnan.
Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en
Ku same mu a https://www.facebook.com/naijcomhausa
Ko a http://twitter.com/naijcomhausa
Idan ka na da wata shawara ko bukatar ba mu labari, a tuntube mu a labaranhausa@corp.legit.ng
Asali: Legit.ng