Innalillahi: An tsinci gawar Manjo Janar Idris Alkali -sojan Najeriya da bace kwanakin baya

Innalillahi: An tsinci gawar Manjo Janar Idris Alkali -sojan Najeriya da bace kwanakin baya

- An tsinci gawar Manjo Janar Idris Alkali -sojan Najeriya da bace kwanakin baya

- An tsinci gawar ne a garin Jos

- Ana zargin yan kabilar Birom ne suka kashe shi

Labarin da muke samu daga majiyoyin mu dai na nuni ne da cewa babban jami'in sojan Najeriyar nan watau Manjo Janar Idris Alkali da muka baku labarin bacewar sa a kwanan baya an tsinci gawar sa.

Innalillahi: An tsinci gawar Manjo Janar Idris Alkali -sojan Najeriya da bace kwanakin baya
Innalillahi: An tsinci gawar Manjo Janar Idris Alkali -sojan Najeriya da bace kwanakin baya
Asali: Facebook

KU KARANTA: Buhari zai sake daukar mutane 5000 aiki

Mun samu cewa dai an tsinci gawar sojan ne a garin Jos ta jihar Filato a kusa da asibitin koyarwa ta jami'ar tarayya dake jihar akan hanyar zuwa matsugunnin jami'ar na din din din.

Legit.ng dai ta samu cewa jami'an tsaron Najeriya ne suka gano gawar ta sa tare da wasu masu sana'ar adai-daita a cikin wani kududdufi dake a garin.

Haka zalika dai majiyar tamu tace ana kyautata zaton 'yan kabilar Birom ne dake a jihar suka kashe su duk da yake dai har yanzu ba samu wani bayani ba daga hukumar sojin kasar game da lamarin.

A wani labarin kuma, Yayin da zabukan shekarar 2019 ke ta kara karatowa, wasu masoyan dan takarar shugabancin kasar dake neman tikitin tsayawa a jam'iyyar adawa ta PDP, Dakta Rabi'u Musa Kwankwaso sun yanka rago tare da addu'o'i ga Allah akan muradin na su.

Kamar yadda muka samu, masoyan na Kwankwaso da galibin su matasa ne sun fito ne daga karamar hukumar Kiru dake a jihar Kano inda kuma suka gudanar da Sallah da saukar al'qur'ani duk domin samun nasarar gwanin nasu.

Latsa wannan domin samun labarai a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/naijcomhausa

Twitter: https://twitter.com/naijcomhausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Authors:
Mudathir Ishaq avatar

Mudathir Ishaq Mudathir Ishaq is the head of the Hausa desk at Legit.ng. He studied Industrial Chemistry as first degree at the University of Abuja, Journalism (CSR Specialization) with the Michigan State University and runs MSc Industrial Chemistry from the Nasarawa State University, Keffi. With more than a decade experience in news reporting and content editing, he has interviewed influential personalities. He can be reached on: mudathir.ishaq@corp.legit.ng