Tsohon shugaban kasa, IBB, ya fadi wanda zai goyawa baya a ‘yan takarar PDP, ya fadi dalili

Tsohon shugaban kasa, IBB, ya fadi wanda zai goyawa baya a ‘yan takarar PDP, ya fadi dalili

Tsohon shugaban kasar Najeriya a mulkin soji, Ibrahim Badamasi Babangida (IBB), ya zabi shugaban majalisar dattijai, Bukola Saraki, a matsayin dan takarar da zai goyawa baya daga cikin masu neman jam’iyyar PDP ta tsayar da su takarar shugaban kasa.

Yanzu lokaci ya yi da zai saka wa mahaifinka abin alherin da ya yi min,” Babangida ya fadawa Saraki a garin Minna, lokacin da ya ziyarce shi jiya, Asabar, a gidansa.

Babangida ya ce Saraki tamkar da ne a wurinsa, kuma zai goya masa baya ya samu nasara a zaben fitar da gwani na jam’iyyar PDP da za a yi a watan Oktoba.

Kai tamkar da ne a wurina. Ba zan manta yadda mahaifinka ya dinga bani shawarwari ba lokacin da nake mulki. Shawarwarinsa sun taimaka min sosai kuma sun kara min karfin gwuiwa a duk wani aiki da zai kawo cigaban Najeriya.

Tsohon shugaban kasa, IBB, ya fadi wanda zai goyawa baya a ‘yan takarar PDP, ya fadi dalili
IBB da Saraki
Asali: Depositphotos

Wannan ziyara da ka kawo min, ziyara ce mai matukar tarihi. Yanzu lokaci ya juya, zan koma mai baka shawara kamar yadda mahaifinka ya bani shawara lokacin ina da ragowar karfi na,” a kalaman IBB.

DUBA WANNAN: Tsohon shugaban PDP ya fita daga jam'iyyar, ya fadi dalili

IBB ya kara da cewar, “manufofinka sun yi daidai da irin manufofina. Ka ambaci abu 3 masu matukar muhimmanci ga kowanne shugaba mai son cigaban jama’a da kasar sa. Manufofinka na son hada kan ‘yan kasa, tabbatar da tsaro da bunkasa tattalin arziki sune abubuwan da nima nayi kokari a kansu lokacin ina mulki.”

IBB ya yabawa Saraki bisa yadda ya hada kan mambobin majalisar dattijai duk da kasancewar sun fito daga jam’iyyu, kabilai da addinai daban-daban.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/naijcomhausa

Twitter: https://twitter.com/naijcomhausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel