Yanzu-yanzu: Ana kishin-kishin din cewa Yusuf Lassun ya koma PDP

Yanzu-yanzu: Ana kishin-kishin din cewa Yusuf Lassun ya koma PDP

Mun fara jin labarin cewa Mataimakin Shugaban Majalisar Wakilan Tarayya Honarabul Yusuf Lassun ya sauya-sheka. Yusuf Lassun ya bar Jam’iyyar APC mai mulkin kasar zuwa PDP bayan ya fadi zaben Gwamnan Jihar Osun.

Yanzu-yanzu: Ana kishin-kishin din cewa Yusuf Lassun ya koma PDP
Mataimakin Shugaban Majalisar Wakilan ya bi Dogara zuwa PDP
Asali: Depositphotos

Idan wannan labari ya tabbata, hakan na nufin Jam’iyyar APC ta rasa duka shugabannin Majalisar Tarayyar Najeriya. A makon da ya gabata ne dai kafar Shugaban Majalisar Wakilai Rt. Hon. Yakubu Dogara ta bar APC.

Hon. Yusuf Lasun wanda shi ne Mataimakin Yakubu Dogara a Majalisa ya tsere daga APC ya koma PDP bayan ya fadi zaben Gwamnan Jihar Osun a karkashin Jam’iyyar APC. Tun a lokacin Lassun a fara kuka da Jam’iyyar.

KU KARANTA: Ana fama da matsaloli a cikin Jam’iyyar APC Inji Lasun

Babban ‘Dan Majalisar ya zargi APC tayi masa rashin adalci bayan da Jam’iyyar ta ba Adegboyega Oyetola tikitin takara a zaben Gwamna da za ayi kwanan nan. Oyetola yana cikin manyan na kusa da Gwamnan Osun Rauf Aregbesola.

Tun a lokacin Yusuf Lasun yace sabon Shugaban APC Adams Oshimhole zai kashe Jam’iyyar. Yanzu dai ‘Dan Majalisar na Osun ya bi Kakakin Majalisa Yakubu Dogara wanda ya kama hanyar ficewa daga APC tun a wancan makon.

Yanzu haka dai APC ba ta rike da shugabancin Majalisa duk da cewa ita ta kafa Gwamnati bayan Sanata Bukola Saraki ya bar APC kwanaki. Dama can dai Sanata Ike Ekweremadu ya dare kujerar sa ne a kan Jam’iyyar adawar PDP.

Mun fara jin labarin cewa Mataimakin Shugaban Majalisar Wakilan Tarayya Yusuf Lassun ya sauya-sheka. Yusuf Lassun ya bar Jam’iyyar APC mai mulkin kasar zuwa PDP bayan ya sha kasa a zabe.

Idan ka na da wata shawara ko bukatar ba mu labari, a tuntube mu a labaranhausa@corp.legit.ng

Ku same mu a https://www.facebook.com/naijcomhausa

Ko a http://twitter.com/naijcomhausa

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Asali: Legit.ng

Online view pixel